Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 29 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 29 ga Watan Agusta, 2019

1. Shugaba Buhari yayi magana game da rufe Bodar Najeriya

Muhammadu Buhari, Shugaban Najeriya a ranar Laraba da ta gabata ya ba da dalilai da ya sa aka rufe bodar Najeriya da ta Jamhuriyar Benin.

Naija New Hausa ta fahimta da cewa shugaban ya bayyana da cewa daya daga cikin dalilan hakan itace yanayin yadda ake shigar da kayakin da doka ta hana, musanman shinkafa.

2. Manufar El-Zakzaky da Iran itace mayar da Najeriya da zaman Kasar Musulunci – FG

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zargi jagoran kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky da wata manufa ta sonkai don kafa Daular Islama a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta kuma bayyana cewa, kungiyar ‘yan Shi’ar suna da karban goyon baya ne daga gwamnatin kasar Iran don cimma wannan buri.

3. APC Ta Sanar da Sabuwar Lokaci da rana don zaben Firamare a Bayelsa

A ranar Laraba da ta wuce, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kai zaben gwamnonin ta jihar Bayelsa zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2019.

Naija News ta tuna da cewa a baya an sanya ranar 29 ga Agusta ne don zaben.

An sanar da canza ranar zaben ne a wata wasika da aka aika wa Shugaban Hukumar Zaben kasa, Farfesa Mahmood Yakubu.

4. Shugaban Majalisar Dattawa, Lawan yayi Alkawarin Tallafawa Tsarin Mulkin Buhari ta karo na biyu

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ba da sanarwar da cewa Majalisar Dattawa ta tara za ta ba da cikakken goyon baya ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari domin samun ingantacciyar rayuwa, wadata da kuma amintar da Najeriya don kyautata rayuwar ‘yan kasa.

“Za mu tabbatar da cewa majalisar ta bada cikakken goyon baya ga shugaba Buhari don cimma burin Mataki na gaba, munsman don amfanin jama’armu da kasarmu,” in ji Lawan a wata bayani da ya bayar a garinsa Gashua, a yammacin ranar Talata da ta gabata a dakin taro, nan jihar Yobe.

5. Osinbajo ya jagoranci Kwamitin Gudanar da Tattalin Arziki

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo a ranar Laraba da ta gabata, ya jagoranci taron kungiyar shugabannin binciken tattalin arziki na wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na 2.

Taken taron itace, “Mataki na gaba”. Batutuwan kasafin kudi kuwa na gudana ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

6. Kotu zata dauki mataki akan kungiyar ‘yan Shi’a a ranar 11 ga Satumba

Bayan ‘yan matsaloli da aka samu da Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wanda kuma aka fi sani da Shi’a, Babban Kotun Tarayya, Abuja ta sanar da ranar 11 ga Satumbar don sauraron karar da kungiyar ta shigar da ke neman kotun ta yi watsi da karar da ta bayar a ranar 26 ga Yuli.

Wannan matakin ya biyo ne bayan Mai shari’a Nkeonye Maha na Kotun ya saurari karar biyu. Babban Lauyan Tarayya, Mista Ayo Apata, SAN, ya nemi karin lokaci.

7. Wasu da ake zargi da zama mahara da bindiga sun sace daliban kwalejin karatun shari’a a ABU

An bayar da rahoton cewa an sace wasu daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a kan hanyar Abuja-Kaduna.

An bayyana da cewa daliban suna shekararsu ta karshe ne a makarantar, a yankin karatun Shari’a a Jami’ar.

8. Shugaba Buhari Ya halarci Taron Kasa da Kasa a Japan

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a yanzu haka yana kasar Japan inda yake halartar taron kasa da kasa na Tokyo karo na 7 kan cigaban Afirka.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa babban taron kasar na gudana ne a Garin Yokohama daga ranar 28 ga Agusta zuwa 30 ga Agusta.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com