Uncategorized
Jami’an Tsaro sun kama wani Mutum mai Shekaru 35 da yiwa ‘Yar shekara 8 Fyade a Kano
Wani mutumi mai shekaru 35 da haihuwa wanda aka bayyana da suna Musa Ibrahim, ya fada a hannun ‘yan sanda a Kano, bisa zargin yiwa wata yarinya‘ yar shekara takwas mai suna Brandy Thomas fyade.
Bisa fahimtar Naija News Hausa a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, an bayyana da cewa lamarin ya faru ne a yankin Rijiyan Zaki da ke cikin birnin Kano, a yayin da mutumin da ake zargi da yin fyaden, wanda ya kasance makwabci ga yarinyar ya yaudari yarinyar mai shekaru takwas da haifuwa da katan din Indomie.
An bayyana cewa yarinyar ta san Ibrahim sosai da kuma hulda bisa zama shiya guda, damar hakan ne kuwa ya sami saukin yaudarar ta zuwa kusurwar wata ginin, inda ya yi nasarar yi mata fyade.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da Wata Mata da ta kashe Maigidanta a Jihar Kebbi don Kokarin koma ga Saurayinta na da
Kodayake, rahotanni sun bayar da cewa wani dangi ga wanda ake zargin, wanda ya zama jami’in hukumar masu shiga da fitar kasa (Immigration Officer), na son yayi amfani da damar Ofishin sa don gudanar da makirci da yin watsi da zargin fyaden.
Da kuwa aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce: “Nan take da rahoton ya kai ga Kwamishinan ‘yan sanda yankin, Ahmed Iliyasu, ya ba da umarnin a yi bincike mai zurfi don gano yanayin da ya haifar da lamarin.”
Ya kara bada haske da cewa an riga an kama Musa Ibrahim da ake zargi da laifin, kuma ana tsare shi, a yayin da ake binciken sa.
”Yarinyar kuwa an riga an kai ta a Asibiti don bata kulawa da binciken yanayin da take a ciki bayan fyaden,”
“A karshen binciken Musa kuma, Kwamishana yayi alkawrin mikar da shi a gaban Kotu don hukunta shi bisa dokar kasa” inji shi.