Connect with us

Uncategorized

El-Zakzaky: IGP ya bada umarnin a Kame dukan Shugabanan ‘Yan Shi’a da ke a fadin Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya  (IGP), Mohammed Adamu, a karshen makon da ta gabata, ya ba da umarnin ga dukan rukunin ‘yan sanda a duk fadin kasar da su fara kame shugabannin kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), da aka fi sani da Shi’a.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa sanarwan ya fito ne bisa umarnin da aka wallafa daga Hedikwatan Rundunar Tsaron zuwa ga dukan Rundunar ‘Yan sanda na Jiha, a ranar 30 ga watan Agusta, 2019, wanda kuwa aka yi gargadi da rashin jinkiri da bin umarnin.

A yayin da ake zancen rushe dukkan tsarin kungiyar da ya taso da tasiri a kasar a baya, IGP ya bayyana da cewa a karkashin sa ba zai bar mambobin Shi’ar damar keta dokar kasa ba.

Wannan matakin ya biyo ne bayan da aka zargi kungiyar ‘yan Shi’a da sanadiyar tashin hankali da farmaki da ya faru a baya a ranar 22 ga watan Yuli tsakanin Jami’an tsaro da ‘yan kungiyar, wanda ya kawo mutuwar mataimakin Kwamishanan Jami’an tsaro da ke a rukunin Tsaro ta birnin Tarayyar Najeriya, FCT Abuja, Mista Umar Usman da kuma wani dan matashi mai da ke hidimar bautan kasar sa (NYSC), Precious Owolabi.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Jami’an tsaro a ranar sun ci nasara da kame ‘yan kungiyar Shi’a 54.

A lokacin da aka bada wannan rahoton ba a samu karban bayani ba daga bakin kakakin yada yawun Jami’an tsaron, FPRO Frank Mba.