Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 2 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 2 ga Watan Satunba, 2019

1. An Kashe Sojojin Najeriya 3 da yiwa 8 A Cikin su Raunuka a Rikici da Boko Haram

Sojoji Uku na Sojojin Najeriya sun rasa rayukansu yayin da wasu 8 suka sami raunuka bayan wata musayar wuta da ‘yan kungiyar Boko Haram a kan hanyar Monguno-Mairari-Gajiram.

Naija News ta fahimci cewa munsayar wutan ya auku ne a ranar Juma’a 30 ga watan Agusta tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da rukunin sojojin na sashi na 3 ta Operation Lafiya Dole wanda ke tsaron Super Camp Monguno.

2. An fara kafa Ruga a Jihar Zamfara

A ranar Talata da ta gabata ne aka tsara shirin Ruga a jihar Zamfara bayan gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ba umarnin da sanarwar fara ayyukan kafa Ruga ga makiyaya a cikin jihar.

Naija News ta fahimci cewa Gwamnan jihar ya ba da wannan umarnin ne a ranar Asabar bayan karbar sabon shirin Ruga daga hannun mai ba da shawara kan ayyukan, Mista Emmanuel Ozigi.

3. A Karshe CAN ta mayar da Martani game da hidimar RUGA

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi watsi da shirin RUGA da aka shirya.

Naija News ta ba da rahoton cewa Fasto Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya baiyana matsayin kungiyar a yayin taron shugabannin Ikilisiyoyi a birnin Legas a ranar Asabar, 31 ga Agusta da ta wuce.

4. Shugaba Buhari Ya dawo kasar Najeriya daga kasar Japan

Shugaba kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Asabar din da ta gabata ya sauka Najeriya a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Naija News ta ba da rahoton cewa isowar shugaba Buhari ya biyo ne bayan kamala Babban Taron Kasa da Kasa na Bakwai kan Ci gaban Afirka (TICAD 7) da ya halartar a Yokohama, kasar Japan.

5. Buratai Ya Ziyarci Dakarun Sojojin Najeriya Bayan Hari

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai ya kai ziyarar bazata ga rundunar Sojojin Najeriya a fagen daga ta Operation Lafiya Dole a Borno.

Naija News ta fahimci cewa ziyarar Burutai ya biyo bayan wani mumunar harin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi ga sojojin a kauyen Gasarwa, kan hanyar Gajiram-Monguno da ke cikin Karamar Hukumar Nganzai na Borno a ranar Asabar.

6. Fasto Adeboye Ya mayar da Martani game da hidimar RUGA

Babban Fasto da Janar na Ikilisiyar ‘The Redeemed Christian Church of God (RCCG)’, Fasto Enoch Adeboye, ya ce ya goyi bayan adawar kungiyar Christian Association of Nigeria (CAN) game da zance a dakatar da hidimar kafa RUGA.

Naija News Hausa ta tuna da cewa kungiyar a baya ta kira ga Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi watsi da shirin RUGA da aka shirya.

7. Shugaban ‘Yan Sanda ya bada umarnin a kama Shugabannin ‘Yan Shi’a A Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ba da umarnin kame dukkan shugabannin kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) a dukkanin jihohin kasar 36.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne bayan da shugaban Jami’an tsaron, Sufeto-janar (IGP), Mohammed Adamu ya ba da umarnin a karshen mako da ta wuce.

8. Abinda Magashi ya fada wa Sojoji a Maiduguri

Ministan Tsaro, Maj.-Gen. Bashir Magashi (Rtd), ya yi alkawarin tsanantawa gwamnatin tarayya don inganta tsarin kulawa ta musanman ga rundunar sojojin Najeriya.

Naija News ta fahimci cewa Magashi (Rtd) ya ce manufar kyautata ga kulawa ga sojojin Najeriyar mataki ne da zai karfafa su da kuma kara masu inganci da karfi wajen yaki da ta’addanci a kasar.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com