Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 3 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 3 ga Watan Satunba, 2019

1. Kotun Koli ta janye Laifuffukan da ake tafkawa a kan Buhari

Kotun daukaka kara wacce ta shigar da karar ga Shugaba Muhammadu Buhari kan ikirarinta game da wata lambar kara (001) da aka gabatar wa Hukumar Zabe (INEC) a ranar 23 ga watan Fabrairu, Kotun Koli ta yi watsi da kararrakin zaben shugaban kasar a yau.

Kotun ta bayyana da amince da cewa karar kan al’amarin shirin zabe ne, kuma an rigaya da kamala zaben watannai da dama, kuma ba a yi jayayya da karar ba tsakanin tsawon kwanaki 14 da aka yanka, saboda hakan karar bata kafu ba.

2. Rikin da Tsananci ga ‘yan Najeriya da ke a South Afrika, a yayin da suka Kona shaguna da Mallakar su

Hare-haren ta’addancin da ‘yan kasar South Afrika ke yi ga ‘yan Najeriyar da ke kasar su ya dauki sabon salo a yayin da ‘yan Najeriya ke cikin mummunan yanayi bisa rahoton cewa an kone shagunonin ‘yan Najeriya da kayaki, da Mallakar su.

Naija News Hausa ta fahimci cewa ‘yan kasar South Afirka din sun kai hari kuma a ofishin jakadancin na Najeriya.

3. Malami Ya Gana Da Shugaba Buhari da Kyari

Bayan nasarar biyan kudi dala biliyan 9.6 da kamfanin Process & Development Development Limited, P&ID, ta samu akan Najeriya, Babban Lauyan Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa, Abuja ranar Litinin.

An hango Ministan Shari’a a yayin da yake kai ziyara ga Shugaba Buhari tare da Shugaban Ma’aikata ga Shugaban Kasa, Mista Abba Kyari.

4. Karar da aka yi kan Sayan Motocin ‘Yan Majalisar Dattawa ta banza ce – inji Kakakin Majalisa

Bayan karar da aka yi a Kotu dakatar da zancen sayan sabbin Motoci ga ‘yan Majalisar Dattawan Najeriya, Majalisar ta bayyana shirin karar da zaman matakin banza.

Kakakin yada yawun Majalisar, Adedayo Adeyeye ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a daren Lahadi da ta gabata.

5. Kotun Koli ta Tsige Memban Majalisar Wakilai na PDP

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a Osogbo, Jihar Osun, ta soke zaben Bamidele Salam, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Ede a majalisar wakilai.

Naija News ta fahimci cewa Kotun ta kori Salam, wanda ke wakiltar mazabar Ede a majalisar wakilai a dandamalin Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), a ranar Litinin, 2 ga Satumbar 2019.

6. Gwamnatin Tarayya ta rufe Babban Hanyar Legas-Ibadan Expressway Don gyara

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) a ranar Lahadin da ta gabata ta fitar da sabon tsarin hanyar bi bisa an rufe babbar hanyar titin Legas zuwa Ibadan don gyara.

Naija News ta fahimci cewa ana son a tabbatar da rufe hanyar ne daga ranar Litinin, 2 ga Satumba, 2019 zuwa ranar Alhamis, 31 ga Oktoba, 2019.

7. PDP ta Bayyana Abinda Kasashen Waje suka yiwa Najeriya A Karkashin Buhari

Babban Jam’iyyar Adawar Najeriya (PDP) ta bayyana ficewar Shugaba Muhammadu Buhari a Japan a taron TICAD 7 da aka yi a matsayin abin kunya.

Jam’iyyar PDP ta yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin nan, da lurar cewa kasashen duniyar da masu zuba jari a kasa sun yi watsi da Shugaba Buhari a lokacin taron.

8. Yadda Muka Taimaka wa FBI ta Kama ‘Yahoo Girl’ – EFCC

An kama wata mace da ake zargi da zamba ta hanyar yanar gizo a jihar Edo sakamakon hadin gwiwa tsakanin Hukumar Yaki da Cin Hanci da kare Tattalin arzikin kasa (EFCC) da Ofishin Binciken Tarayya (FBI).

Naija News ta samu gane da cewa Macen da ake zargi, ko da shike ba a bayyana sunanta ba, tana yin aikin ne tare da hadin gwiwar takwarorinta da ke a kasar Turai.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com