Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 5 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 5 ga Watan Satunba, 2019

1. Najeriya tayi Watsi da Taron Kasa da Kasa kan Tattalin Arziki

Najeriya ta kauracewa Taron Tattalin Arzikin duniya kan Afirka wanda zai gudana a garin Capetown, South Afirka tsakanin ranar 4 ga Satumba zuwa 6 ga Satumba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Gwamnatin Tarayyar ta daukin matakin ne saboda harin ƙunar baƙin wake a kan ‘yan Najeriya a kasar South Afrika hade da sauran baki a kasar.

2. Wada Ya ci Nasarar zaben Firamare ta PDP a Jihar Kogi kan neman kujerar Gwamna

Rahotanni da suka isa ga Naija News sun nuna cewa Engr. Musa Wada a ranar Laraba da ta gabata ya bayyana a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben gwamna a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi.

Naija News ta fahimci cewa Musa Wada ya ci nasarar hakan ne da yawar kuri’u 748 don lashe zaben firamaren Jam’iyyar.

3. Babban Kwamishanan Najeriya a South Africa ya mayar da Martani game da zancen Katange ‘Yan Najeriya a Kasar

Babban wakilin Najeriya a kasar South Afirka, Amb. Kabiru Bala, ya ce ba gaskiya ba ne da cewa kasar ta katange kofar ta ga ‘yan Najeriya da suka zo yin rajistar korafinsu kan harin ba aka yi wa ‘yan uwan su.

Naija News ta fahimci cewa Bala ya fadi hakan ne yayin tattaunawa ta wayar tarho da ‘yan jaridar Najeriya daga Pretoria, kasar South Afirka a ranar Laraba, 4 ga Satumba.

4. Najeriya Ta yi kirar Gagawa ga Ambasadan Najeriya a South Afirka

Naija News ta karbi rahoton cewa anyi kirar kalubalanta ga Babban Kwamishanan da ke wakilcin ‘yan Najeriya a South Afirka, Ambasada Kabiru Bala, da ya dawo gida don bayyana abin da ke gudana a kasar.

Naija News ta fahimci cewa an sake kiran Ambasada Bala ne sakamakon harin ta’addancin da aka yiwa ‘yan Najeriya a South Afirka.

5. Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da ke Bincike akan Wadume ya Mutu

An tabbatar a rahoto da cewa jami’in ‘yan sanda da ke aiki tare da Rundunar Leken Asiri (IRT) ta rundunar ya mutu a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Ibi Taraba.

An kuma bayar da rahoton cewa wasu jami’an ‘yan sanda hudu da wasu mutane biyar da ake zargi sun samu raunuka a hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 6 na yamma, ranar Litinin, 2 ga Satumba.

6. Gwamnatin Tarayya ta bayyana Ranar Da Zata bayar da Kasafin kudin 2020 ga Nass

Ministar Kudi, Malama Zainab Ahmed, a ranar Laraba, ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga Majalisar Dokokin Kasar a karshen watan Satumba.

Ministar ta sanar da hakan ne a cikin jawabinta na farko a wani babban taron tattaunawa game da bayar da gudummawar Jini a kasar Abuja, ranar Laraba da ta gabata.

7. Xenophobic: Kamfanin MTN ta ba da umarnin rufe ofisoshi a duk fadin kasar Najeriya

Kamfanin Sadarwa ta kasar South Afirka, MTN ta rufe ofisoshinta da ke a Najeriya sakamakon ramuwar gayya da aka yi kwanan nan wanda ya biyo bayan harin ‘yan South Afirka kan ‘yan Najeriya.

Kamfanin sadarwar wanda ta tabbatar da rufewar Ofisoshinta a ranar Laraba, ta ce ta samu tabbacin cewa ‘yan Najeriya na kai hari a cibiyoyinta da ke a Legas, Ibadan, da Uyo.

8. Jam’iyyar APC ta bayyana mai nasara ga zaben Firamare ta neman kujerar Gwamna a Bayelsa

A ranar Laraba da ta wuce, David Lyon ya fito da lashe zaben fidda gwani a zaben firamare ta Jam’iyyar APC a kujerar Gwamna ta jihar Bayelsa.

Naija News ta fahimci cewa jam’iyyar APC a Bayelsa ta dage kan zaben fidda gwani na kai tsaye don zabar dan takarar da zai tashi tuta a zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba a Bayelsa.

Karanta kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa a koyaushe.