Connect with us

Uncategorized

Abinda Tsohon Shugaba, Goodluck Jonathan ya fada game da Kisan ‘Yan Najeriya a South Africa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya nuna bacin rai da takaici da abin da ke afkuwa a kasar South Africa. Jonathan ya kuwa yi kira da karshe irin wannan hare-haren da ke afkuwa a kasashen Afrika duka.

Naija News Hausa ta gane da cewa bayanin tsohon shugaban ya fito ne a yayin wata gabatarwa da yayi a ranar Alhamis da ta gabata lokacin da yake gabatarwa a wajen taron zaman lafiyar tarayyar kasa da aka yi a Sao Tome da Principe, bayan ganin irin karuwar mumunar hari da ‘yan kasar South Afrika ke yiwa ‘yan kasar Najeriya da ke zaune a can.

A cikin bayanin Jonathan, ya fada da cewa “Idan lallai ana son ci gaba ta musanman, ya zan dole a karfafa ‘yan Afrika gaba daya da su kula da juna da kuma koyi yi mu’a’mala da ‘yan uwa duka a cikin Soyaya da hadin kai”

“Ba kamata a ce an bar irin wannan tashin hankali da matsalar ya ci gaba ba a Afrika, inda kasa ko wata yanki ba za ta ita neman taimako ba daga sauran kasashe.”

“Karuwa da ci gaba zata samu ne kawai idan shugabannan kasa sun iya gudanar da ayukan su yadda ya kamata da kuma tsaya kai tsaye don tallafa wa al’umar kasar” inji jonathan.