Connect with us

Uncategorized

Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi ya Mayar da Martani game da Ziyararsa da Fayemi, El-Rufai a kasar South Afirka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanusi, Fayemi, El-Rufai sun yi Liyafa a South Afirka a yayin da ake Kashe ‘yan Najeriya a kasar

An gano mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a yayin da yake Liyafa a kasar South Afirka tare da Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, Gwamnan Jihar Ekiti da Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna a yayin da ake kisa da tsananta wa ‘yan Najeriya a kasar.

Wannan ya bayyana ne a lokacin da ‘yan Najeriya suka daga murya game da bayyanar Jim Ovia da sauran’ yan Najeriya, har da tsohuwar minista Oby Ezekwesili a taron tattalin arzikin duniya na Afirka 2019, wanda ke gudana a Cape Town, kasar South Afirka.

Sarkin Sanusi, a yayin da yake mayar da martani game da zancen, ya ce “Dagaske ne na isa kasarar South Afrika a safiyar ranar Talata da ta wuce, na kuma halarci Taron Tattaunawa akan Tattalin Arzikin Kasa a ranar Laraba, ba da sanin abin da ke afkuwa ba”

“Na tafi kasar ne da guri biyu; Daya daga ciki kuwa don gayyatar da wani abokina ya yi mani ne, na biyun kuma ta kai na ne don halartar wata hidimar da aka bukace ni da bada gabatarwa, da ni da kuma wadanda suka ziyarceni mun kuwa kauracewa taron da zarar da muka sami labarin abin da ke afkuwa”

“Da zarar da muka ji abin da ke afkuwa kan ‘yan Najeriya muka kaurace da janye kanmu daga taron, kuma a haka na dawo gida” inji Sanusi.