Connect with us

Uncategorized

Wata Yarinya ta Haska wa Kanta Wuta don Saurayinta ya gaza Biyan Sadakin da aka Yanka Masa

Published

on

at

advertisement

Wata yarinya ‘yar shekara goma sha bakwai (17) da haihuwa wacce aka bayyana da suna Aisha mai zama a yankin Albarkawa a cikin garin Gusau ta jihar Zamfara, a ranar Lahadi ta haska wa kanta wuta sakamakon cewa Saurayinta ya kasa ga iya biyan sadakin aurenta saboda rashin kudi.

Bisa bayani da Maƙwabcin A’isha ya shaida wa Aminiya, ya bayyana da cewa ta yanke hukuncin kashe kanta ne bayan da ta samu labarin cewa mai bidanta da aure tun da dadewa ya kasa iya biyan kudin sadakin iyayenta suka yanka masa domin shirya bikin auren.

Ya ce; “mahaifiyar Aisha sun yi kira ga mai neman ta da aure da ake kira da suna Umar da ya gabatar da kansa ga dangin nata don shirin auren sa da diyarsu, amma saurayin ya fada wa iyayenta cewa bashi da kudin naira dubu goma sha bakwai (N17,000) da zai iya biya kamar yadda mahaifin Aisha ya bukace shi da biya.”

“Da jin hakan ne ta kawo wani gallon man fetur da kuma kwalin Ashana. Ta kuwa wanke kanta da man fetur din ta kuma tsinki sandar ashana ta haska wa kanta wuta, nan take cikin ‘yan mintoci kuwa ta kame da wuta”

Ko da shike an iya gane da cewa ko kamin Aisha ta haska wa kanta wuta kanuwar ta tayi kokarin hanata da daukar mumunar matakin amma ta ki bin shawarar.

“Kanwarta tayi jayayya da ita akan hakan amma ta sha karfin kanwar, da kuwa ta gaji da jayayya da ita sai tayi kokarin yin kirar taimako daga mazauna unguwar, amma kamin a samu wanda ya iso ta rigaya da kyasta ashana”

“A yayin hakan ne wasu mazauna suka hanzarto da cecon ranta da mutuwa a cikin wutar.”

Abin takaici Uban Aisha ya furta da cewa a halin da yake a ciki bai da kudin da zai iya kaita a asibiti don bata cikakken kulawa daga kamuwar wutan.

Aminiya ta bayar da rahoton cewa anyi anfani ne da magungunan gargajiya don kula da Aisha ga samun sauki daga konewar wutan.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Wata Mata ta kashe Maigidanta a Jihar Kebbi don Kokarin komawa Saurayinta na da.