Connect with us

Labaran Najeriya

NextLevel: Ka Sauka daga Shugabanci – PDP sun gayawa Buhari

Published

on

at

PDP Ta Mayar da Martani Bayan Lai Mohammed Ya Roki ‘Yan Najeriya da suyi wa Shugaba Buhari Hakuri

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka daga shugabancin kasar nan da nan.

Babbar jam’iyyar adawar ta yi wannan kiran ne a lokacin da take mayar da martani game da wani faifan bidiyo da ke fitowa a kafafen sada zumunta inda Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya yi kirar hakuri ga ‘yan Najeriya kan takardar shaidar WAEC ta shugaban kasar.

Kalli bidiyon a kasa, inda Lai Mohammed ya Roki ‘Yan Najeriya da yafe wa Buhari akan Takardan WAEC;