Shugaba Buhari ya Ba da umarnin a dawo da ‘Yan Najeriya Daga kasar South Afirka

Bayan ganin irin mumunar harin ta’addancin da ‘yan Najeriya suka fuskanta a kasar South Afirka, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ya gana da hukumomin kasar kan yadda za a kawo karshen hare-haren ta’addancin da ake kaiwa ‘yan Najeriya.

Shugaban ya kuma amince da dawowa da ‘yan Najeriya da ke son komawa Najeriya daga kasar ta jirgin sama da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta samar a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News Hausa ta kuma samu rahoton cewa Mutum daya ya mutu, wasu biyar kuma suka jikkata a Johannesburg, babban birnin kasar South Afirka, a wani sabon harin ta’addanci na kiyayya da aka yi wa ‘yan Najeriya a kasar.

Bisa rahotannai da aka bayar ta hannun manema labarai, abin ya faru ne a ranar Lahadi, 8 ga Satumbar, bayan da jamiā€™an tsaro suka yi artabu da masu satar kayakin mutane a cikin barkewar sabon rikicin.