Connect with us

Uncategorized

Karanta Dalilin da Ya sa Hukumar NECO ta ki Sakin Sakamakon Jarabawan Dalibai a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jarrabawa ta kasar Najeriya da aka fi sani da NECO, ta ki sakin sakamakon jarabawar watan Mayu da Yuni wanda daliban makarantun gwamnati a jihar Neja suka yi, saboda gazawar gwamnatin jihar wajen biyan bashin da ke kanta a Majalisar.

Naija News Hausa ta fahimci cewa an saki Sakamakon jarabawar NECO na watan Mayu da Yuni tun ranar 27 ga watan Agusta 2019, amma ɗalibai da yawa ba za su samu damar diban sakamakon jarabawar ta su ba a jihar saboda matsalar bashin da ake bin gwamnatin Jihar.

Bisa rahoton da manema labarai ta gidan jaridar Daily Trust suka bayar da kuma ganewar Naija News, wannan ya haifar da matsalar hana yawancin dalibai a jihar da samun damar shiga Manyan Jami’o’i don karasa karatun su, musanman yin jarabawar UTME.

Ko da shike Gwamnatin Jihar ta bada tabbacin cewa lallai a gaskiya suna da biyan bashin kudi naira Miliyan N470 ga Hukumar NECO.

Bisa bayanin Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Malam Abubakar Aliyu da manema labarai, ya bayyana da cewa gwamnatin jihar ta riga ta biya Naira Miliyan Dari da Hamsin (N150m) a cikin bashin da ake bin ta.

Ya yi kira ga Hukumar jarrabawar da ta ba wa daliban damar samun sakamakon su musamman wadanda lokaci ya kawo da zasu yi amfani da sakamakon jarrabawar UTME din su, yayin da ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar zata cika ga daukan nauyin biyar sauran bashin da ke a kanta.

Naija News na da sanin cewa Gwamnatin jiha ta saba da biyan kudin jarabawar NECO da WAEC ta dalibanta tun a baya a duk lokacin da akwai isashen kudin yin hakan a asusun jihar.

KARANTA WANNAN KUMA: An yi Kusa da Karshe Babban Hanyar Minna zuwa Suleja