Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 17 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 17 ga Watan Satunba, 2019

1. Buhari ya ambaci majalisar ba da shawara kan tattalin arziki

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nada majalisar ba da shawara kan tattalin arziki (EAC) ga gwamnatin “Next Level”.

Naija News ta fahimci cewa sabuwar majalisar ba da shawara kan tattalin arziki (EAC), ta kunshi hadin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Farfesa Chukwuma Soludo da Mista Bismarck Rewane a matsayin mambobi.

2. IGP Adamu ya ayyana Abuja da zama yanki mafi tsari a dukan Duniya

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya ce a Abuja, Babban birnin Tarayyar Najeriya ya kasance da tsaro, amintacce ba ta kuma karkashin kowane irin katangewa na matsalar tsaro.

Naija News ta fahimci cewa shugaban ‘yan sandan ya yi wannan magana ne a kan matsalar hare-hare da aka yi a baya, musamman akan hanyar Kaduna-Abuja.

3. Wakilan kasar South Afirka Sun Gana da Shugaba Buhari A Abuja

Manzannin musamman da Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar South Afirka ya turo ga Najeriya sun yi wata ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke a Aso Rock Villa, birnin Abuja.

Ka tuna da cewa sabbin hare-haren ta’addanci a kasar South Afirka akan ‘yan Najeriya da wasu kasashen Afrika ya haifar da hargitsi da tashin hankali a kasashen Afirka.

4. Seun Onigbinde ya yi Murabus da Matsayin da shugaba Buhari ya Sanya shi

Jagora da shugaban BudgIT, Seun Onigbinde ya yi murabus daga matsayin da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya shi, watau, mai ba da shawara a fannin Fasaha a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na kasa.

Naija News ta ruwaito da cewa Onigbinde ya gabatar da hakan ne a cikin sanarwar ya sanya hannu a ranar Litinin.

5. Kotu ta yanka hukunci a kan Gwamna Makinde

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ranar Litinin, ta bayyana nasara ga Gwamna Seyi Makinde na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Naija News ta gane da cewa nasarar gwamna Makinde a kotun zaben gwamnoni jihar Oyo ya biyo ne bayan da Adebayo Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya shigar da kara akan Makinde a zaben gwamna da aka yi a ranar 9 ga Maris a jihar.

6. Za a ci gaba da Binciken da Kalubalantar Fayose a ranar 21 ga Oktoba

Zargin Binciken Makirci da Kudi kimanin Naira biliyan 9.9 da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, zai ci gaba a ranar 21 ga watan Oktoba a gaban wata babbar kotun tarayya da ke a jihar Legas.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Hukumar Yaki cin Hanci da Rashawa da kuma kare tattalin arzikin kasa (EFCC) na gurfanar da Fayose ne akan badakalar kudi biliyan 9.9 da aka karkatar.

7. Nnamdi Kanu na IPOB ya isa Switzerland gabanin ganawa da UN a kan Biafra

Shugaban kungiyar Asalin ‘yan Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya isa Geneva, Switzerland gabanin “muhimmiyar ganawarsa” tare da wasu jami’an Majalisar Dinkin Duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta samu tabbacin cewa shugaban IPOB din ya isa Geneva a Switzerland a ranar Litinin, 16 ga Satumbar kafin ganawarsa da jami’an Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran zai gabatar da jituwa ga Jamhuriyar Biafra a gaban Majalisar Dinkin Duniya.

8. Sowore Yayi sabuwar kirar Gafartawa ga Kotu

Shugaban Kanfanin Dilancin Labarai da aka fi sani da Sahara Reporters, da kuma dan takarar kujerar shugaban kasar a zaben watan Fabrairu 2019, Omoyele Sowore ya bukaci a sake shi da komawa ga ayukan sa.

Naija News ta fahimci cewa jagoran Zanga-zangar #RevolutionNowmovement din ya samar da takardar neman belin ne a gaban Babbar Kotun Tarayya ranar Juma’a da ta gabata.

9. Sojoji Sun yi Munsayar Wuta da ‘yan Kungiyar Boko Haram a Jami’ar Maiduguri

Wasu da ake zargin su da zama ‘yan kungiyar Boko Haram, a ranar Lahadi sun kai hari a babban Jami’ar Maiduguri, da ke jihar Borno ta Arewa a Najeriya.

An fahimci cewa ‘yan ta’addar, sun yi kokarin mamaye harabar jami’ar ne ta shingen bayanta amma rundunar Sojojin Najeriya suka tare su da munsayar wuta.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com