Connect with us

Uncategorized

Babban Bankin Najeriya ta bullo da sabbin manufofi na cajin ‘yan Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Bankin Najeriya (CBN) ta ba da umarnin aiwatar da wani sabon tsari na manufofinta wanda zai kai ‘yan Najeriya ga biyan wasu ‘yan kudade don bayar da ajiyar kudade a asusun bankuna.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne a cikin wata sanarwa wadda aka bayar a ranar 17 ga Satumbar, 2019, wacce Daraktan Babban Bankin CBN, Sam Okojere, ya umarci bankunan da su aiwatar da manufar daga raanar 18 ga Satumba 2019.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar Jarrabawa ta kasar Najeriya da aka fi sani da NECO, ta ki sakin sakamakon jarabawar watan Mayu da Yuni wanda daliban makarantun gwamnati a jihar Neja suka yi, saboda gazawar gwamnatin jihar wajen biyan bashin da ke kanta a Majalisar.

Ko da shike Gwamnatin Jihar ta bada tabbacin cewa lallai a gaskiya suna da biyan bashin kudi naira Miliyan N470 ga Hukumar NECO. Amma dai bisa bayanin Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Malam Abubakar Aliyu da manema labarai, ya bayyana da cewa gwamnatin jihar ta riga ta biya Naira Miliyan Dari da Hamsin (N150m) a cikin bashin da ake bin ta.