Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Bar Najeriya Yau zuwa kasar Amurka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Naija News Hausa, Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Labaran Najeriya a Yau, Labaran Hausa, Shugabancin Kasar Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 22 ga Satumba, ya tafi New York, kasar Amurka don halartar taro na 74 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA74).

Naija News na da sanin cewa an bude Taro na 74 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniyar (UNGA74) ne a ranar Talata, 17 ga Satumba.

Ka tuna a baya Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa a Najeriya a zaben shugaban kasa na 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya yi barazanar cewa yana da isassun hujjoji da za su kori Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki a Kotun Shugaban Kasa.

Gidan Labaran nan ta fahimta da cewa a karshe Kotun daukaka kara kan zaben Shugaban kasar (PEPT) a ‘yan kwanaki da suka gabata, ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararar su, Atiku Abubakar suka gabatar a kotun.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce hukuncin da kotun daukaka karar shugaban kasa ta gabatar nasara ce ga ‘yan Najeriya da suka dage da tabbatar da zabensa a karo na biyu a karagar mulki.