Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 25 ga Watan Satumba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 25 ga Watan Satumba, 2019

1. Majalisar dattijai ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin CBN, AGF Malami, Sauran su akan kwangilar P&ID $ 9.6b

Majalisar dattijan Najeriya ta 9 ta yi kira ga Babban Lauyan Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan ci gaban da aka samu a kan jayayyar kudi na dala biliyan 9.6 tsakanin Najeriya da hukumar P&ID.

Naija News ta gane da cewa Majalisar dattijai karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawan ta gayyaci AGF Malami da gwamnan babban bankin kasa (CBN) tare da sauran hukumomin a wata ganawar tsiri a ranar Talata, 24 ga Satumba.

2. Buhari ya canza mukamin Minista Festus Keyamo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Festus Keyamo, Ministan Jihadin Yankin Neja-Delta ga ma’aikatar kwadago da aiki.

Naija News ta bayar da rahoton cewa, Keyamo ya canza mukami ne tare da Tayo Alasoadura, Ministan Ma’aikata, wanda ya koma Ma’aikatar Neja Delta a yanzu sanadiyar matakin Buhari.

3. Atiku da PDP sun gabatar da sabon Kara a gaban Kotun daukaka karar Shugaban Kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, da jam’iyyarsa sun shigar da karar su game da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke a kotun koli.

Ka tuna da cewa kotun kolin a baya ta yi watsi da karar da Atiku da PDP suka yi kuma aka tabbatar da zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

4. Kotu ta bada Hukuncin Yanci ga Sowore

Kotun da ke kula da karar kamfanin jaridar Sahara Reporters da dan takarar shugaban kasa da ya shiga zaben fidda gwani, Omoyele Sowore a ranar Litinin sun ba shi beli.

Naija News ta tuno da cewa an gurfanar da Sowore a gaban kotun kwanaki da suka shige a kan tuhumar cin amanar kasa da alaƙa da zanga-zangar ‘juyin juya halin’ da aka shirya.

5. Majalisar dattijai ta sanya ranar da za ta fito da Kwamitoci

Majalisar dattijai ta 9 ta Najeriya ta sanya ranar Laraba, 25 ga Satumbar, don ta kafa da gabatar da sabon kwamiti

Naija News ta samu tabbacin hakan ne bayan wata ganawa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan a wani taron tisiri ranar Talata.

6. PDP Gargadi Shuganci da ta Binciki Osinbajo Akan wata Biliyan N90biliyan da aka Fyauce

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babban Jam’iyyar Adawa a Najeriya ta yi kira da a binciki badakalar kudaden da suka kai biliyan N90 daga Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya (FIRS) wacce aka ambata sunayen manyan mutane a cikin shugaban kasa.

Jam’iyyar PDP ta kalubalanci Buhari da fadin cewa kada ya boye gaskiyar, “mumunar cin hanci da rashawa da ya shafi manyan jami’an da ke cikin wannan gwamnatin, kamar yadda ta saba yi a baya.”

7. Masu zanga-zanga sun hari Majalisar Jihar Legas da neman a Binciki Ambode

Masu zanga-zangar sun bayyana a ranar Talata, da yawan su sun afkawa majalisar dokokin jihar Legas da zanga-zanga da neman a bincike tsohon gwamnan Jihar, Akinwunmi Ambode.

Naija News ta fahimci cewa masu zanga-zangar karkashin kungiyar Legas Van Van (LYV) sun yi zanga-zangar ne zuwa gaban majalisar dokokin jihar Legas, dauke da tambura daban-daban da kuma rera taken hadin kai.

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa