Connect with us

Uncategorized

Sanata Kwankwaso ya tallafawa daliban Kano 242 ga zuwa Karatu a Turai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dalibai 234 daga kananan hukumomi 44 a jihar Kano da sun kammala karatun digiri na farko sun ci amfanin tallafin karatu a kasashen waje a jagoranci da taimakon Rabiu Kwankwaso.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa daga cikin dalibai 234, wasu zasu yi karatun su ne a manyan jami’a hudu da ke a kasar Indiya, a yayin da kuma wasu zasu tafi kasar Sudan don tasu karatu.

Tallafin karatun ya isa ne ga daliban a karkashin Kwankwasiyya Development Foundation, kungiyar siyasa ta tsohon gwamna jihar, Rabiu Kwankwaso.

A lokacin da Kwankwaso ke jawabi a wajen bikin murna ga wadanda suka amfana da tallafin, a nan gidan sa na Kano, ya ce;  “234 daga cikin daliban za su yi karatun digiri na biyu da ake cewa Masters a Kimiyya, Fasaha, da Al’adu a Indiya, yayin da takwas daga cikinsu za su yi karatun addinin Musulunci da Larabci a Sudan.”

“Kungiyar Kwankwasiyya ta riga ta biya dukkan kudade hade da kudin koyarwa, masauki, ciyarwa, da inshora ga jami’o’in,”

Ya kara da cewa tuni an amintar da tikitin dawowar su gida bayan kamala karatu duka daga jami’o’in.

Tsohon Gwamnan da kuma Sanata da ya wakilci yankin Kano ta Tsakiya ya gargadi daliban da su kasance jakadu na gari a zamansu a kasashe biyun, da kuma ba da tabbacin cewa ba da dadewa ba kungiyar zata fara shirye-shirye dalibai ba zasu tafi karatun a karo na biyu.