Connect with us

Labaran Najeriya

Ina Kuwa Tausaya wa Tinubu – Mike Ozekhome

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Babban Lauyan fafutukar Kasa, Mista Mike Ozekhome, ya bayyana cewa yana tausayawa Shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Mike, Mai kare hakkin dan adam ya bayyana cewa rukunonin da ke a cikin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari suna shirin tsige Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne, bayan da suka yaudare shi da amfani da shi wajen rarraba Tradermoni ga ‘yan kasuwa kamin babban zaben da ya gabata.

Wannan furci ta Mike Ozekhome na fitowa ne bayan wasu cece-kuce da ya biyo matakin da shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatinsa ta dauka na raba Osinbajo da wasu makamai da ya jagoranta.

Ka tuna, kamar yada Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnan sa da irin abokin takara da ya ke da shi, watau hadewarsa da Farfesa Yemi Osinbajo.

Naija News Hausa gane da bayanin Buhari ne a yayin bayan hadarin jirgin sama da Farfesa Yemi Osibanjo ya yi a ranar 2 ga Watan Fabrairu, 2019 a lokacin da yake hanyar zuwa Jihar Kogi don gudanar da yakin neman zabe a Jihar.

“Na Gode wa Allah da kare mataimaki na, Farfesa Yemi Osibanjo daga hadarin jirgin sama da ya yi a ranar Asabar da ta gabata,”

“Ina yaba wa mataimaki na da kuzari, kokari da kuma irin karfin lamirin zuciya da ya ke da shi, harma da iya ci gaba da hidimar yakin neman zaben bayan hadarin da ya faru da shi a ranar” in ji fadin Buhari.