Connect with us

Uncategorized

Cutar Yellow Fever Ya Kashe Akalla Mutane 16 a Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbin rahoton cewa kimanin mutane 16 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a cikin jihar Bauchi ‘yan kwanakin nan.

An samu tabbacin hakan ne bisa bayanin Shugaban zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar, Dakta Rilwanu Mohammed ga Gidan Talabijin na Channels.

A cewarsa, karuwar lambar mutanen da suka mutun ya zamana ne bayan kin amincewar da ‘yan yankin suka yi na karban allurar rigakafi a yayin gudanar da rigakafi a duk fadin jihar.

Naija News Hausa ta sanar watannai kusan bakwai da suka shige yadda Cutar Lassa Fever ya kashe mutane 10 a Jihar Plateau da wasu yankunan kasar Najeriya.

Da Dokta Rilwanu ke karin haske, ya bayyana cewa, fiye da mutane 119 ne ake tuhuma da kamuwar cutar a Jihar. Ko da shige 20 daga cikin su aka tabbatar da su dauke da cutar, a haka kuma 16 daga cikin su sun riga sun mutu.

Ya karshe da cewa hukumar jihar tana shirin shiga duk wuraren da aka tabbatar da barkewar cutar don zagayan kofa da kofa da kuma taimaka masu da magunguna, musanman kulawa ta gaske.