‘Yan sanda sun Tabbatar da Karban Yancin Mahaifiyar Samson Siasia

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa Madam Beauty Ogere, mahaifiyar Samson Siasia, tsohon kocin ‘yan wasan Super Eagles, ta samu yanci daga hannun ‘yan Garkuwa.

Don bada tabbacin hakan, a ranar Lahadi Mista Asinim Butswat, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Sufeto Janar na ‘yan sandan yankin, ya ce rundunar ‘yan sanda za ta fitar da sanarwa ta musanman game da hakan ba da jimawa ba.

Naija News Hausa ta sanar a cikin wata rahoto a baya da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Malama Beauty Ogere Siasia, Maman Mista Samson Siasia, tsohon kocin ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya, a jihar Bayelsa.

Naija News ta fahimta da cewa wannan itace karo na biyu da ‘yan garkuwa ke sace Maman Siasia, da aka bayyana da tsawon shekaru 76 ga haifuwa.