Connect with us

Uncategorized

Kotu ta yanka Hukunci karshe a kan zaben Ganduje

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Kano da ke zaune a Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin Gwamnan Jihar.

Naija News ta fahimta da cewa Kotun daukaka karar ta jihar Kano ta gabatar ne da hukuncin karshe game da zaben gwamnan Kano a ranar Laraba, 2 ga Oktoba.

Wannan ya biyo ne bayan da Kotun ta dakile dukkan karar da Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka gabatar, na kalubalantar ayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna jihar a zaben ranar 9 ga Maris a jihar, wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta jagoranta.

Naija News Hausa ta gane da cewa Mai shari’a Halima Shamaki, shugabar kwamitin mutane uku, a cikin hukuncin da aka karanta na sama da awanni 3 a babbar kotun jihar, a cikin karamar hukumar, Kano, ta yi watsi ne da karar da PDP ta yi na neman soke nasarar Ganduje a zaben gwamna na ranar 9 ga Maris.

Ka tuna a baya da cewa Gwamnatin Jihar Kano a jagorancin Abdullahi Ganduje ta sanar da bayar da Daji Biyar ga Makiyaya don aikin Kiwo a Jihar.