Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 3 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 3 ga Watan Oktoba, 2019

1. Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Shirya da Maido Da Toll Gate a Titunan Tarayya

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta rigaya da fara tsare-tsare da matakin dawo da Toll Gates a kan manyan hanyoyin tarayya.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimta da hakan ne a yayin da Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, yayin da yake gabatar da jawabai ga ‘yan majalisar dokokin jihar bayan majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta gana da Shugaba Buhari a taron da ya jagoranta a zauren majalisar, fadar shugaban kasa, Abuja, babban birnin Najeriya.

2. Shugaba Buhari Ya Bar Abuja Don ziyarar kasar South Afirka

Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya a safiyar ranar Laraba, 2 ga Oktoba, ya bar reshen shugaban kasa ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Najeriya don ziyarar kasar South Afirka.

Naija News ta fahimci cewa Shugaban tare da mabiyan sa sun tafi ziyarar kasar ne na tsawon kwanaki uku.

3. Kotu ta Ba da hukuncin Karshe A Zaben Gwamna Ganduje

Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Kano da ke zaune a Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin Gwamnan Jihar.

Naija News ta fahimta da cewa Kotun daukaka karar ta jihar Kano ta gabatar ne da hukuncin karshe game da zaben gwamnan Kano a ranar Laraba, 2 ga Oktoba.

4. Osinbajo Ya baiyana Tsahihiyar biyayya da yake da shi Ga Shugaba Buhari

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi alkawarin biyayya mara matuka ga Shugaba Muhammadu Buhari da Tarayyar shugabancin Najeriya.

Naija News ta fahimta da cewa Osinbajo ya nuna yin watsi da jita-jitan cewa akwai wata rashin jituwa da ke gudana a fadar Shugaban kasa.

5. Dalilin da yasa Aka Ce inki Karɓan aiki daga hannun Buhari – Soludo

Tsohon gwamnan Babban Bankin tarayyar Najeriya, Farfesa Charles Soludo ya bayyana cewa kwanan baya wani abokin nasa ya shawarce shi da ya ki karbar nadi daga Shugaba Muhammadu Buhari.

Soludo ya yi wanna furcin ne a lokacin da ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin masu jawabi The Platform 2019, taron shekara da shekara, wanda Cibiyar Kiristoci ta Duniya ke shiryawa a Legas.

6. Kotu ta Isar da hukuncin karshe akan zaben Tambuwal

Kotun daukaka karar zaben Sakkwato a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta tabbatar da zaben gwamna Aminu Tambuwal na Jam’iyyar PDP, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Naija News ta sanar da fahimtar cewa Kotun daukaka kara a Sakkwato ta gabatar da hukuncin karshen ne game da zaben gwamna na Sakkwato a ranar Laraba, 2 ga Oktoba.

7. Babban Bankin CBN ta ba da wata sabuwar Umarni Bankuna kan Bayar da Lamuni

Babban bankin tarayyar Najeriya (CBN), ta bai wa bankunan kasuwanci ranar 31 ga Disamba, 2019 don su kara adadin kudaden da za su ba da rancen daga kashi 60 zuwa 65.

Sabuwar umarnin ta fito ne a cikin wata wasika wacce Daraktan banki da Kulawa, Bello Hassan ya rattaba hannu ga dukkan bankunan, “Matakan da za a bi don inganta bayar da rance ga ainihin tattalin arzikin Najeriya.”

8. Kotu ta Isar da Hukunci na qarshe akan zaben Lalong

Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Filato da ke zaune a jihar Filato a arewacin Najeriya, a ranar Labara ta tabbatar da zaben gwamna Simon Lalong na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Naija News ta fahimta da rahoton ne bayan da Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Filato ta zartar da hukuncin karshe game da zaben gwamnonin Filato a ranar Laraba, 2 ga Oktoba.

Naija News reports that the Plateau State Election Petition Tribunal delivered the final judgment on the Plateau governorship election on Wednesday, October 2.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a Naija News Hausa a ko yaushe.