Connect with us

Uncategorized

An Kama Mutane 21 da ke Samar da Magunguna ga Boko Haram a Jalingo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta sanar da kama akalla mutane 21 da ake zargi da samar da magunguna ga ‘yan kungiyar Boko Haram.

Naija News ta fahimci cewa, an kama wadanda ake zargi da hakan ne bayan da ma’aikatan hukumar NDLEA suka fada ga wata tasha da ke a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, inda mutanen ke sayar wa ‘yan ta’addan magungunar.

A cikin Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta yau, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ya yaba wa maza da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa kokarinsu na tabbatar da tsaro a kasar.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma bayyana bukatar sake yin nazari kan karfafa tsarin tsaron kasar Najeriya domin samun kyakkyawan sakamakon yaki da ta’adanci da fatauci a kasar.