Connect with us

Labaran Najeriya

An zabi Buhari ne don ya gyara kurakuran da PDP tayi bawai Yin Gunaguni ba – Galadima

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dattijo da jigo a Jam’iyyar PDP, Buba Galadima, ya fada da cewa an zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne don gyara matsalolin da ake zargin gwamnatin jam’iyyar PDP da ita bawai don korafi ba.

A cikin wata hirar da ya yi da New Telegraph, tsohon mashawarci ga shugaban kasar ya nuna rashin jituwa da wadanda ke zargin shugabancin Jam’iyyar PDP da sanadiyar matsalolin kasar a wa’adin da suka gabata.

Naija News Hausa ta ruwaito a watannan baya da cewa Kakakin yada yawu ga lamarin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubaka, dan takaran shugaban kasa ga zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP, Buba Galadima ya karyata kuri’un da hukumar INEC ta gabatar kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Ka tuna a baya da cewa Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wasu bayanai game da yanayin da ya shafi amincewarsa da ya yi na karban kadara ga zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2015 a Najeriya.

Jonathan ya fada da cewa bai taba yin nadama ba a kan matakin da ya dauka ga daukar kadara da amincewa da nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

“Banyi wata Nadama ba ga amincewa da nasarar Muhammadu Buhari a zaben 2015, kuma har gobe ina shirye don daukar irin wannan matakin idan hakan zai haifar da zaman lafiya a kasa” inji Jonathan.