Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 7 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 7 ga Watan Oktoba, 2019

1. An zabi Buhari ne don ya gyara kurakuran da PDP tayi bawai Yin Gunaguni ba – Galadima

Dattijo da jigo a Jam’iyyar PDP, Buba Galadima, ya fada da cewa an zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne don gyara matsalolin da ake zargin gwamnatin jam’iyyar PDP da ita bawai don korafi ba.

A cikin wata hirar da ya yi da New Telegraph, tsohon mashawarci ga shugaban kasar ya nuna rashin jituwa da wadanda ke zargin shugabancin Jam’iyyar PDP da sanadiyar matsalolin kasar a wa’adin da suka gabata.

2. Dalilin da yasa bai kamata PDP ta Nemi jayayya da hukuncin Kotu ba – Babban jigon APC

Shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyyar da ke mulkin jihar Kaduna sun gargadi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da cewa kada ta yi jayayya da shigar da sabon kara kan kalubalantar nasarar gwamna Nasir El-rufai a matsayin gwamnan Jihar Kaduna a karo ta biyu.

Naija News ta sanar da cewa shuwagabannin jihar sun shawarci babbar jam’iyyar adawar, PDP, da su je su shirya domin babban zaben 2023 maimakon ‘bata lokaci da kalubalantar nasarar da kuma yin kara a kotu.

3. Majalisar Kwara ta Ba da Dalilai Na Kwace Mallakar Saraki

Majalisar Dokokin jihar Kwara ta gabatar da dalilan da ya sa aka kwace Alimi Chalet da wata mallakar fili da ake kira Ile Arugbo wacce ake zargin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da ita.

Majalisar a cikin wata sanarwa da kamfanin Naija News ta karba a ranar Lahadin da ta gabata, sun bayyana cewa sun bada umarni kwace mallakar ne saboda sun gane da cewa mallakar ta gwamnatin jihar ne, kuma babu wata hujja da ta nuna cewa Saraki ya biya su.

4. Wasu Kungiya na shigar da Zargi ga Gwamnan Bankin Tarayya, da kuma yin kara ga shugaba Buhari

Wata kungiya a Kudu maso Gabashin Najeriya, Zikist-Buharist Movement (ZBM) ta zargi gwamnan Babban Bankin Tarayyar Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da karkatar da yankin Kudu Maso Gabas da Kudu maso Yamma a cikin shirye-shiryen shigar da kara na bankin koli.

Kungiyar ta gabatar ne da karar a kan Emefiele a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Rt. Hon. Stanley Ohajuruka da Sakatare, Godwin Onwusi, ZBM a Enugu a ranar Lahadi, 6 ga Oktoba da ta gabata.

5. IPOB Ba zata Samar maku da Shugabancin ba a 2023, ACF ya gargadi Iyamirai

Sakatare-janar na kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), Anthony Sani, ya gargadi ‘yan kabilar Igbo da kada su yi amfani da kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) don barazana ga Arewa a kan kujerar shugabancin ta shekarar 2023.

Naija News ta ruwaito cewa dattijon shugaban Jam’iyyar APC din, Dr Chukwuemeka Ezeife, a wata hira da wata jaridar kasar ya ce Igbo na iya mara wa IPOB baya idan aka hana su shugabancin kasar a 2023.

6. 2023: Dalilin da Yasa Ba Zai Yiwu Ba ‘Yan Igbo su Shugabanci Kasar Najeriya ba – Wabara

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Adolphus Wabara ya yi ikirarin cewa babu damar Shugabancin kasar Najeriya ga Iyamirai a shekarar 2023.

Ya bayyana da cewa an riga an sanya tsare-tsare, raunanar karfi da tsananci ga Nndigbos a hidimar siyasa, musanman a fifikon kabilanci da burin neman shugabancin kasar a cikin shekaru hudu masu zuwa.

7. Dalilin da yasa Buhari ya ki Mayar da Wuta ga ‘Yan ta’addar South Afrika – Shugabancin Kasa

Fadar Shugaban kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ki daukar fansa a kan harin da ‘yan ta’addan South Afrika suka yiwa ‘yan Najeriya a kasar saboda yana ganin jituwa zai fi kyawu kan al’amarin.

Babban Mataimakin Shugaban kasa na Musamman akan Sadarwa a layin yanar gizo, Garba Shehu ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

8. Boko Haram: Gov Zulum Ya Gabatar da Malamai 30 Domin Yin Addu’a

Gwamna Babagana Zulum ya yi zabin wasu mazauna 30 a Birnin Makkah na Saudi Arabiya don yin addu’ar kawo karshen matsalar harin Boko Haram a jihar Borno.

Wannan rahoton ya fito ne a sanarwan mai taimakawa gwamnan kan yada labarai, Isa Gusau.

9. PDP ta kalubalanci Shugabancin Kasa da bayani kan Kamun Nasir

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nemi fadar shugaban kasa da ta mayar da martani kan rahotannin kame Nasir Danu, mai rikon amanar Shugaba Muhammadu Buhari, da aka sanar.

Naija News ta sanar da cewa an kama Nasir Danu ne a tashar jirgin sama ta Heathrow, United Kingdom, saboda zargin kirar fasfot mara daidaita da kuma zargin hadahadar kudi.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa