Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 8 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 8 ga Watan Oktoba, 2019

1. Shugaba Buhari ya Shawarci Al’ummar Kasa da Zuba jari ga kayayyakin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki shugabannin bangarorin kamfanonin gwamnati da ta dayantaka a Najeriya da su kara ga watsar da jarinsu a kayayyakin da ake kira a Najeriya.

Naija News ta samu labarin cewa Buhari ya yi kirar hankalin ‘yan Najeriya a taron kolin tattalin arzikin Najeriya karo na 25 (NES25), inda ya gargadi shugabannin kamfanoni da su mayar da hankali ga zuba jarin su ga kasuwanci a kasar don raya da karfafa tattalin arzikin kasar.

2. Sarki Sanusi Ya Bayyana Yaduwar Jama’ar Najeriya a Matsayin karin Raunana ga Kasar

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi (II), ya baiyana yawan jama’a a Najeriya a matsayin abin da zai raunana tasiri da ci gaban kasar bisa ganin cewa nauyi zai karu kan gwamnatin kasar.

Sarkin Sanusi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron kwamitin tattalin arzikin Najeriya karo na 25 da ake gudanarwa yanzu haka a Abuja, birnin Tarayyar Najeriya.

3. Kotu ta yanke hukuncin Karshe kan zaben Ortom

Kotun Sauraron karar neman kujerar gwamna a jihar Benue, da ke a Makurdi, babban birnin jihar, ta tabbatar da zaben gwamna Samuel Ortom a matsayin mai tabbacin nasara ga zaben Jihar.

Naija News ta ruwaito cewa Ortom ya tsaya takarar a dandamali na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

4. Mafi karancin albashi: Gwamna Fayemi Ya Bayyana Matsayin Gwamnonin Kan Biyan Albashin

Gwamnan jihar Ekiti da kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Kayode Fayemi a ranar Lahadi da ta gabata ya ce, gwamnoni sun dauki matsaya kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

A cewarsa, akwai banbanci tsakanin karin albashin mafi karancin albashi na kasa da kuma duba batun albashi na gaba daya, kuma gwamnoni suna da fahimtar hakan.

5. #SexForGrades UNILAG ta dakatar da Dr Boniface, Malami da aka gane da halin Lalaci

Cibiyar Babban Jami’ar UNILAG ta Jihar Legas ta dakatar da Dakta Boniface Igbeneghu, malamin sashen fasaha a Jami’ar, saboda laifin lalata da aka gane da shi.

Naija News ta ba da rahoton cewa Dr Boniface, wanda ke zaman fasto a Cocin Foursquare Gospel Church da ke Legas, ya bayyana a cikin wani shirin bidiyo na mintina 13 da BBC Africa ta saki a ranar Litinin.

6. 2023: Edwin Clark Ya Bayyana Mafi Kyawun Dan takara da Zai zama Shugaban Najeriya

Dattijo da kuma shugaba ga kungiyar ‘yan Ijaw, Cif Edwin Clark, ya baiyana goyon baya ga dan takarar Igbo (Iyamirai) ga shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Dan siyasar ya baiyana cewa al’ummar Igbo sun cancanta da samar da shugaban Najeriya na gaba.

7. Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed

Kotun zabe a jihar Bauchi ta baiyana goyon bayanta ga Sanata Bala Mohammed a matsayin gwamnan jihar.

Naija News ta bayar da rahoton cewa, alkalin kotun, Mai shari’a Salihu Salisu, ya yi watsi da karar da Mohammed Abubakar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka gabatar na jayayya da nasarar Bala.

8. Kotu Ta Tabbatar Da Kwace Miliyan N280m Da aka gane da Invictus Obi

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta ba da umarnin karban kudi kimanin Miliyan N280,555,010.65 da aka samu a cikin asusun bankunan ta kamfanoni biyu da Obinwanne Okeke, wanda aka fi sani da suna Invictus Obi ya mallaka.

Naija News ta fahimci cewa kotun ta ba da izinin karbe kudin ne da aka samu a asusun ajiyar kamfanin bisa zargi da ake da jagoranta.

Ka tuna da cewa Okeke na fuskantar gurfana a kasar Amurka kan zargin satar dala miliyan 11 bayan zargin sa da wasu ‘yan Najeriya 77 suka yi.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa