Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 9 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 9 ga Watan Oktoba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na 2020 ga Majalisar Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da kasafin kudi na N10.729 tiriliyan 2020 ga taron hadin gwiwar Majalisun kasar Najeriya domin amincewa da ita.

A cewar alkalumman, an kasafta tiriliyan N2.46 don manyan ayyuka a kasar bisa tsari da danganci farashin $57 ta gangar mai da VAT 7.5%.

2. Ina Fama da Zazzabi sanadiyar yawar Aiki da ni ke yi – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiyana da cewa yana cikin fama da zazzabi, ya kuma danganta rashin lafiyar ga yawar aikinsa a matsayin Shugaban Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai ta Naija News na ba da rahoton cewa Shugaban kasar ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

3. Gwamna ya umarci ‘Yan Sanda da su Harbe duk wanda ya Tsare shi da Darukan sa a hanya

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ba da umarni ga Jami’an tsaron sa a cewa daga yanzu, su harbe duk wanda ya tsare motar sa a kan tafiya.

Gwamnan ya bayyana da cewa duk wanda ya mutu daga irin wannan harbin, to dokar kasa ta amince da hakan.

4. Wadume: Kwamitin DHQ ta Ba da rahoto Akan Kashe-kashe a Taraba

Kwamitin Shugaban kasa wanda Babban Hafsan Tsaro, Janar Abayomi Olonisakin, ya jagoranta na a shirye don binciken kisan wasu ‘yan sanda uku da aka sanya ga rukunin tsaro ta (IRT) yayin kamen Hamisu Bala Wadume.

Naija News ta bayar da rahoton cewa ana zargin sojojin Najeriya da kashe ‘yan sandan a Taraba, ranar 6 ga watan Agusta, 2019.

5. Biafra: Nnamdi Kanu ya daga murya da cewa ‘Mutuwa na jiran ‘yan Biafra’

Shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana takaicin cewa mutuwa tana jiran “dukkan ‘yan asalin Biafra” da ke neman yanci ga kafa Jamhuriyar Biafra idan ba su tashi tsaye ba don neman hakinsu.

Naija News ta bada rahoton cewa shugaban IPOB din, Kanu yayi wannan tsokaci ne yayin gabatarwansa a shafin watsa labaran Radiyon Biafra a ranar Litinin, 7 ga Oktoba.

6. Majalisar Zartarwa ta Kasa ta Gabatar Shirin Ciki Aiki a Kan Kasafin kudin 2020

Kwamitin majalisun biyu na majalisar zartarwar kasar za ta kammala aikin tantance da kimantawa kan kasafin kudin shekarar 2020 kafin karshen watan Oktoba, in ji shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan.

Shugaban Majalisar, Ahmed Lawan, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata yayin gabatar da kasafin na 2020 da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar a zauren Majalisar Tarayya a Abuja, babban birnin Najeriya.

7. ‘Yan Garkuwa sun Sace kimanin Mutane 9 a Abuja

Naija News ta karbi rahoton sabuwar harin mahara da bindiga a hanyar Abuja, ranar Litini da ta gabata.

Rahoton ya bayar da cewa kimanin mutane 9 ne mahara da bindigar suka sace a Pegi, wata karkara da ke a karamar hukumar Kuje, Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, a safiyar ranar Litini, 7 ga watan Aktoba da ta gabata.

8. Toll Gates: Kungiyar MASSOB tayi watsi da Tsarin Shugaba Buhari bisa sabon Tsari da aka fitar

Kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra (MASSOB), ta zargi gwamnatin tarayya da shirin karin zaba ga mutanen yankin.

Naija News ta fahimta da cewa masu fafutukar kafa kasar Biafra sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari kan jagorantar gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen gina wasu kofofi 56 a shiyyar Kudu maso Gabas da jihohi 5 kacal.

9. ‘Yan Hari da bindiga sun sace Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya biyu A Jihar Ribas

Wasu ‘yan sanda biyu da aka sanya ga tsaro a rukunin ‘yan sandan Najeriya da ke a jihar Rivers, sun fada a hannun wasu ‘yan garkuwa a shiyar Ngor, hedikwatar karamar hukumar Andoni ta jihar.

Naija News ta fahimci cewa, an sace jami’an ‘yan sandan Najeriyar ne a ranar Litinin, 7 ga Oktoba, aka kuma tafi da su inda ba wanda ya san da shi.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa