Connect with us

Uncategorized

EFCC sun Taras da Kudi Miliyan N65,548 a Ofishin INEC ta Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa da kare tattalin arzikin kasa (EFCC), da ke a Yankin Jihar Sakkwato a ranar Laraba ta aiwatar da zagayen bincike a ofishin Hukumar gudanar da Zabe ta jihar Zamfara, inda suka ci karo da dunbun kudi miliyan N65.548.

Naija News Hausa ta fahimta bisa rahoto da cewa an gano da kudaden ne a cikin wasu manyan akwatin ajiya wanda harsasun bindiga ba zai iya fashewa ba, a nan cikin ofishin Ofisa kula da shiga da fitar kudi na hukumar INEC a jihar.

Wannan zagayar binciken ya fito ne bayan da wani ma’aikacin hidimar zabe a jihar ya tayar da zargin cewa jami’an hukumar sun cire wani bangare na kudin tallafin da ya kamata a bayar ga malaman zabe a babban zaben da ya gabata.

A cewar mai karar, INEC a jihar Zamfara ta biya ma’aikatanta kudi N9,000, bisa wasu jihohi kamar Sakkwato ta biya ma’aikatansu N12,000.

Ofisan yada yawu ga hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana da cewa kudin da suka ci karo da ita a ofishin INEC a matsayin kudade ne da aka bayar musanman don aiwatar da aikin zaben da ta gabata, musanman wajen samar da kayakin zabe, kamarsu kujeru, tebura da runfar zabe, harma da albashin malaman zabe, wanda hukumar ta ki amfani da dukan kudaden a yadda ya kamata.