Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 10 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 10 ga Watan Oktoba, 2019

1. Majalisar dattawan Najeriya sun muhawara kan kasafin kudin shekarar 2020

Naija News ta ba da rahoton cewa majalisar dattijan Najeriya a ranar Laraba da ta gabata ta fara muhawara kan ka’idoji na kasafin kudin shekara ta 2020.

Ku tuna da cewa, a ranar Talata da ta wuce ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 na N10.33trillion zuwa gaban majalisar dokokin kasar.

2. Next Level: Shugaba Buhari Yayi sabon Alkawari Ga ‘Yan Najeriya

A ranar Laraba da ta wuce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ziyarar wasu daga cikin ministoci da suka yi aiki tare da shi a lokacin mulkin soja, tsakanin watan janairu 1984 zuwa Agusta 1985, a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Yayin da yake karbar bakuncin Shugaban, Buhari ya tuno da yadda suka gudanar da al’amura a lokacin, saboda gwamnatin soja ce a lokacin, ya kuma yi alkawarin da cewa “a wannan lokacin, musanman wa’adi na na karshe a matsayin zababben shugaba, zan tabbatar da gudanar da shugabanci da kulawa da kowane.”

3. Shugaba Buhari Ya Gana Da Kwamitin Ba da Shawara kan Tattalin Arziki A Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya gana da shugaba da kuma membobin kwamitin ba da shawara kan tattalin arzikin kasar a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja, birnin tarayyar kasa.

Naija News ta fahimci cewa taron ya soma ne a misalin karfe 11:30 na safiya a nan ofishin Shugaban kasar.

4. Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta gabatar da ranar ganawa kan Mafi karancin albashi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da shugabannan Kungiyar kwadagon Najeriya, sun shirya babban ganawa a ranar 15 ga Oktoba, don daukar cikakkiyar mataki kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

Naija News ta samu tabbacin rahoton ne ta bakin Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige, a wata sanarwa da ya bayar a ranar Laraba bayan wata ganawa Hukumar (TUC) da kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC).

5. #MainaGate: EFCC ta karbi Umarnin kara Tsayar da Maina

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma kare Tattalin Arziki Kasa (EFCC) ta karbi sabon yarda daga kotu akan kara tsare tsohon Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan fansho, Mista Abdulrasheed Maina da dansa Faisal, a yayin da ake kammala bincikensa.

Kotun Koli ta Babban Birnin Tarayya da ke a Bwari, ta ba da umarnin ne a ranar 7 ga Oktoba, 2019, bayan wata takaddama da hukumar EFCC ta yi.

6. Dalilin da yasa Kasafin kudin 2020 ba zai yiwu ba – Sanata Abaribe

Shugaban majalisar dattawan Najeriya marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce kasafin kudin shekarar 2020 da aka gabatar ba zai zama da saukin aiwatarwa ba, saboda biyan bashi ya wuce kudaden manyan ayukan kasar.

Naija News ta bayar da rahoton cewa, sanatan da ke wakilcin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar ya yi wannan tsokaci ne a yayin muhawara kan manyan ka’idojin kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Laraba.

7. Guru Maharaj Ji Ya Bayyana wa Atiku abinda zai yi wa Buhari

Jagora da shugaban kafa rukunin ruhaniya na kauna daya (One Love Family), Sat Guru Maharaj Ji ya bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar da ya guji kalubalancin sakamakon hukuncin Kotu kan zaben shugaban kasar da ta wuce.

Maharaj Ji a maimakon haka ya shawarci Atiku ya ci gaba da rayuwarsa tare da tallafawa Shugaba Buhari a cikin aikin gina kasar.

8. #SexForGrades: A qarshe, ASUU ta mayar da martani akan Laktaran da aka kama da da laizin Zina

Hadaddiyar Kungiyar Malaman Ilimi ta Jami’o’i (ASUU) ta yi kira da a gudanar da bincike da kuma ladabtarwar da malamin da aka samu da laifin cin amanar dalibai mata, watau “Jima’i don maki”.

Naija News ta bayar da rahoton cewa, BBC ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wasu malamai daga Jami’ar Legas da na Jami’ar Ghana bisa zarginsu da cin zarafin wata ‘yar jarida da ta boye kurwa a matsayin daliba a makarantun.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa