Uncategorized
Kiwon Lafiya: Amfanonin Ganyan Zogale a Rayuwar Dan Adam
Naija News Hausa ta kulla da cewa akwai ‘Ya’yan itatuwa da Ganye da dama da ke da amfani, kwarai da gaske a jikin dan Adam. Amma, wayewa da sabuwar zamani da muke ciki ya sa da yawa an manta da wadannan, musanman taimakawa da suke yi a jikunan mu, kamar yadda Allah ya bada sani da ganewa ga masu binciken amfanonin wadannan itacen, ganyakinsu da kuma diyan itacen.
A Yau zamu kafa baki ga ‘yan bayanai kadan akan amfanin GANYAN ZOGALE
Zogale wani Icce ne da aka fi samun sa a yakunan Arewacin Najeriya, da kuma wasu kasashe a Afirka. Shi Zogale daga bawar iccen har ga ganyensa yana da tasirin amfanin kwarai da gaske ga al’umma.
Kadan daga cikin Amfanin Ganyan Zogale, wanda a turance ake kira da suna ‘Moringa Leaf’, Su ce kamar haka;
1. Maganin Olsa (ULCER):
Shi Ganyan Zogale akan iya dafa shi hade da zuma asha kamar yadda ake shan shayi don maganin Olsa
2. Maganin Kurajen Jiki:
Idan an hada garin Zogale da Man Zaitun, sai a shafa shi kan wajen da kuraje ke fitowa daga jiki.
3. Zubar Jini Ga Yankewa ko Sarewa:
Ga wanda ya yanke ko ya samu rauni daga sarewan karfe, irin wannan ciwo, idan aka shafa danyen ganyen Zogale, da yaddan Allah jinin zai tsaya, za a kuma samu sauki.
4. Maganin Ciwon Kai:
Idan akwai mai jin ciwon kai na damun sa, Idan aka samu danyen ganyen zogale, sai a murza a kuma shafa akan goshi, wannan zai kawo sauki da yaddan Allah.
5. Yawan Fitsari (Diabetes):
Ga duk wanda ke fama da yawan fitsari wanda a turance ake kira da ‘Diabetes’, Da yaddan Allah ya rinka shan furen zogale hade da citta kamar shayi.
6. Maganin Shawara:
Idan aka iya dafa ganyen zogale aka kuma hada tareda kanwa kadan, shan wannan zai magance ciwon shawara a gurguje.
7. Ciwon Ido:
Ga duk mai fama da Ciwon Ido ko ta Kunne, Idan har aka diga ruwan danyen zogale, lallai hakan zai warke.
8. Hawan Jini:
Idan ana Sanya garin zogale acikin abinci, lallai wannan yana maganin Hawan jini dakuma kara kuzari ga dan Adam.
9. Maganin Sanyi:
Ita Ganyan Zogale Idan har aka tafasa furensa hade da Albasa, akasha kamar yadda ake shan shayi, tau lallai yana maganin sanyi jiki.
10. Maganin Ciwon Hanta ko Koda:
Ita ganyen zogale, idan aka daka da ‘ya’yan ‘baure, akan iya shansa da nono ko kunu don maganin ciwon hanta ko koda.
Kadan kenan ciwon amfanin Ganyan Zogale a jikin dan Adam. Allah ya sa a dace.
Don kari da Cikakken Labaran Najeriya, Ka latsa shafin Hausa.NaijaNews.Com a koyaushe.