Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Tuesday, 15 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Tuesday, 15 ga Watan Oktoba, 2019

1. Yajin Aiki: Kungiyar Kwadagon Najeriya da Gwamnatin Tarayya sun Gana akan mafi karancin albashi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya kan aiwatar da sabon matakin biyan mafi karancin albashi na kasa N30,000.

Naija News ta samu labarin cewa ganawar ta fara ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin, a yayin da Ministan kwadago da aikin kasa, Dakta Chris Ngige ya jagoranci taron.

2. Babbar Ofisan Kwastam yayi Magana game da Budewar Boda da aka Rufe

Kwamishina-Janar na Kwastam a Najeriya, mai ritaya Col. Hameed Ali ya bayyana lokacin da za a bude bodar shiga da fitar kasar Najeriya ga kasashe da ke zaman makwabta ga kasar, da kuma irin kayakin da yakamata su shigar da fitar a kasar.

A cewar Ali, ba za a janye haramcin shigowa da fitar da kaya daga bodar kasar ba har sai an samu yarjejeniya tsakanin kasar da kasashe makwabta kan nau’ikan kayayyakin da yakamata su shigar da kuma ficewar a Najeriya.

3. Kwamitin Da Aka Sanya Don Sauraron Karar PDP Ba ta Kafu ba – Kotun Koli

Kotun koli ta karyata rahotannin da Kungiyar Hadin Kan Jam’iyyun siyasa (CUPP) ta yi ta cewa kotun ta sanya alƙalai ta musanman don sauraron karar da Atiku Abubakar da Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi kan zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta ba da rahoton cewa, Kakakin CUPP, Ikenga Ugochinyere ya zargi babban alkalin Najeriya (CJN) Mohammed Tanko da shirya makirci ga jerin alkalan kotun kolin.

4. Kingsley Moghalu ya yi Murabus da YPP, ya bayyana Mataki ta gaba

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP), Farfesa Kingsley Moghalu ya yi murabus daga zaman mamban jam’iyyar.

Moghalu ya bayyana sabon matakin na sa ne a layin yanar gizon nishadarwa ta Twitter a ranar Litinin, amma bai bayyana sabuwar jam’iyyar siyasar da ya shiga ba.

5. Bai Yiwuwa Najeriya ta Zama kasa mai Jam’iyya Daya Kacal – CUPP

Kungiyar Hadin gwiwar Jam’iyyun siyasa ta Najeriya (CUPP) ta mayar da martani ga ikirarin da Jam’iyyun All Progressives Congress suka yi cewa Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya daya.

Kungiyar hadin gwiwar a cikin wata sanarwa da ta saki a bakin kakakinta, Imo Ugochinyere, ta ce abin dariya ne cewa Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu, yana zancen cewa jam’iyyun adawa sun kare a kasar Najeriya.

6. Jamhuriyar Nijar Ta Gudanar da Zanga-zanga, Da kuma hana Shigar da Shinkafa a Najeriya

Jamhuriyar Nijar, wacce ke makwabtaka da kasar Najeriya ta hana fitar da shinkafa daga kasar zuwa Najeriya sakamakon rufe bodar da Gwamnatin Najeriya ta yi.

An sanar da hakan ne a ranar Litini a birnin tarayya, Abuja, ta bakin Kwamandan hukumar kwastan na Najeriya, Col Hameed Ali (rtd) a wata taron tattaunawa da manema labarai.

7. Dan Jarida Ya Bayyana wata Sirri Game da ‘Yan Sandan Najeriya

‘Yar jaridar nan mai bincike, Fisayo Soyombo, ta sha alwashin bin diddigin cin hanci da rashawa a tsarin shari’ar da ke gudana a Najeriya, kuma ta sha makonni biyu a tsare – kwanaki biyar a gidan ‘yan sanda sannan takwas a zaman fursuna a gidan yarin Ikoyi.

Naija News Hausa ta samu ganewa da cewa ‘yar jaridar tayi hakan ne don samun cikakken sani da irin cin hanci da ke gudana kangin jami’an tsaron kasar.

8. Jonathan, IBB da Obasanjo zasu raba Biliyan N2.3

Tsohon Shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Babangida (IBB), za su samu tarin daman N2.3 biliyan a karkashin kasafin kudin shekarar 2020.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin N10.33 tiriliyan ga babban taron majalisar zartarwar kasar ranar Talata, makon da ya gabata.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa