Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Sama Ta Najeriya Sun Rusa Gidan Taron ‘Yan Boko Haram a Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoto da ke isowa ga Naija News Hausa ya bayyana da cewa rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun rushe wata rukunin ‘yan Boko Haram da ke a Boboshe, a karkarar da Dajin Sambisa ta ke a nan Borno.

An bayyana da cewa wannan wajen da Sojojin suka suka rusa da Bam wajen hadin taro ne ga ‘yan ta’addan Boko Haram.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne a wata sanarwa da Daraktan Hurda da Jama’a na hukumar NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bayar a ranar Litini a birnin Tarayyar kasar, Abuja.

A bayanin Daramola, rundunar sun kadamar da harin ne ga ‘yan ta’addan a ranar Lahadin da ta gabata da hadin gwiwar rukunin tsaron ta Operation Lafiya Dole.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta sanar da kama akalla mutane 21 da ake zargi da samar da magunguna ga ‘yan kungiyar Boko Haram.

Mista Daramola ya gabatar da cewa wajen da suka rusa da bam ne shugabanan Boko Haram kan taru don bada umarni ga mambobinsu kamin su tafiyar da duk wata hari ga gwamnati ko ga al’umma.

Ya kara da cewa lallai hukumar NAF na shirye don karin kuzari ga tabbatar da cewa sun shawo karfin dukan rukunin ta’addanci a Arewacin kasar.