Connect with us

Labaran Najeriya

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Rage Albashin Gwamnoni da Wasu Shugabannai a Kasar

Published

on

at

Ministan kwadago da daukar Ma’aikata a kasar Najeriya, Mista Chris Ngige, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na duba albashin ma’aikatan siyasa a kasar hade da ta gwamnoni.

Naija News bisa rahoto da manema labarai suka fitar, Ministan yayi wannan sanarwar ne a Abuja ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin membobin kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomin Najeriya (NULGE) yayin wata ziyarar da suka yi a Ofishin sa.

Ngige ya jaddada da cewa za a yi nazari da albashin shugabannan siyasa nan jin kadan, kamar yadda aka yi a shekarar 2011 da ta gabata.

“Shin me Gwamna ke yi da albashin haɗari da kuma tallafin izinin zaɓe? na lura da cewa duk waɗannan abubuwan za a bincika,” inji Mista Chris a sanarwan.

KARANTA WANNAN KUMA; An zabi Buhari ne don ya gyara kurakuran da PDP tayi bawai Yin Gunaguni ba – Galadima