Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 16 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 16 ga Watan Oktoba, 2019

1. Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadagon Kasar ta kai ga Karshen Ganawa, An kuma dauki sabon Mataki

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar wata tawaga wacce Ministan kwadago, Chris Ngige ya jagoranta, ta kawo karshen ganawarta da kungiyar kwadago game da sabon mafi karancin albashi na ma’aikata.

Naija News ta fahimta da cewa bayan ganawar kungiyar kwadagon da Gwamnatin tarayya kamar yadda aka sanar a baya da taron akan sabon mafi karancin albashi, su biyun ba su kare taron da yarjejeniya ba.

2. An Fitar da Sabuwar Karar Rashin Amincewa da Nasarar Buhari a Kotun Koli

Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta shigar da wata sabuwar kara a Kotun Koli don kalubalantar sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta rahoto cewa HDP ta roki kotun kolin da maido da hukuncin da aka yanke ranar 3 ga Oktoba, wanda bisa wata dalili aka yi watsi da karar da Jam’iyyar ta shigar game da zaben Buhari.

3. Yadda Buhari ya Inganta Halin tsaro a Najeriya – Lai Mohammed

Ministan Watsa Labarai da Al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya baiyana cewa kokarin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ke yi akan yankunan da ke fuskantar matsalar tsaro ya taimaka kwarai da gaske, akwai alamun ci gaba, inji shi.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da nasa jawabin a yayin taron baje koli na musamman kan harkokin tsaro wanda ma’aikatar sa ta shirya kan kokarin Gwamnatin Tarayya da na gwamnatocin Arewa maso Yamma don magance rashin tsaro a yankin.

4. PSC ta yanke hukunci kan Jerin daukar sabbin ‘yan sanda

Hukumar ‘Yan Sanda (PSC) ta Najeriya ta yi watsi da jerin sunayen manema aikin tsaro a rundunar ‘yan sanda ta Najeriya (NPF) da aka fitar.

Naija News ta bayar da rahoton cewa zancen yin watsi da batun ya fito ne a wata sanarwa da shugaban manema labarai da hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya bayar a Abuja, babban birnin Najeriya.

5. Majalisar Dattawa ta Bai wa MDAs ‘Yan Kwanaki don kare Kasafin Kudi

Majalisar dattijan Najeriya ta bai wa kwamitocin da aka sanya umarnin kare kasafin kudin shekarar 2020.

Naija News ta sanar da cewa wannan zancen na zuwa ne bayan kammala muhawararsu game da ka’idojin kasafin kudin shekara ta 2020.

6. Duba Dalilin da zai iya sa a tsige Yahaya Bello daga zaben Kogi

Mai yiwuwa a dakatar da Yahaya Bello, gwamnan jihar daga takarar gwamna a ranar 16 ga Nuwamba idan kotu ta yanke hukuncin hakan.

Wannan ya biyo ne bayan karar da Natasha Akpoti, ‘yar takara daga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta gabatar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, da neman a fitar da Bello daga takaran bisa dalilan yin rijista sau biyu.

7. ‘Yan Najeriya Zasu Bada N3,000 Don Sabunta katin zama dan kasa, N5,000 Domin Munsaya

Hukumar Jagorancin Katin Zama Dan Kasa (NIMC) ta ce ‘yan Najeriya za su biya N3,000 ga Remita, hanyar yanar gizo, don sabunta katunan zama dan kasa, da kuma biyan dubu biyar (5,000) don musanya katin.

Naija News ta samu tabbacin sanarwan ne kamar yadda hukumar ta fitar da jerin sakonnin ta shafin twitter (@nimc_ng) a ranar Talata.

8. Buhari ya nemi amincewar majalisar dattijai don biyan Yahaya Bello N10.069bn

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa wasika ga Majalisar dattijan Najeriya, ta neman amincewa da biyan N10.069 biliyan a matsayin yarjejeniyar cika alkawarin gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello.

Zancen ya fito ne a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aika wa majalisar dattawan Najeriya.

9. Boko Haram: Ndume Ya Bayyana Yawan Sojojin da Aka kashe, da Kuma aka binne a Borno

Sanata Ali Ndume, Sanatan da ke wakilcin APC a Borno ta Kudu a ranar Talata ya ce sojojin Najeriya 840 da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kashe daga shekarar 2013 har zuwa yau an binne su a makabartar Soja da ke cikin Maiduguri, Jihar Borno.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawar yayin zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce adadi bai hada da sojojin da ‘yan Boko Haram din suka kashe ba, da kuma aka binne su a wasu kaburburan sojoji da ke wasu sassan Arewa maso Gabas.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa