Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 18 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 18 ga Watan Oktoba, 2019

1. Kungiyar Kwadago ta kai ga Yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya kan Warancin Albashi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da kungiyoyin kwadago a kasar sun cimma matsaya kan tsarin aiwatar da shirin N30,000, sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata na kasa.

Naija News ta ba da rahoton cewa Gwamnatin Tarayyar da kungiyar kwadagon sun cimma yarjejeniya kan karuwa ga kashin albashin ma’aikata a sakamakon sabon mafi karancin albashi na N30,000 a daren ranar Alhamis.

2. Shugaba Buhari Ya Amince Da N10bn Ga Filin jirgin saman da ke a Enugu

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da ware kudi N10bn don haɓaka filin jirgin saman Akanu Ibiam, da ke a Jihar Enugu.

A cewar shugaban wanda ya bayyana hakan ta hanyar shafinsa nishadarwan sa ta Twitter a ranar Alhamis, da cewa kudin za a yi amfani ne da shi don gyara ga filin jirgin saman.

3. Ministan Kudi ya bayyana Dalilin da yasa Najeriya ke Aron $3bn daga bankin duniya

Malama Zainab Ahmed, Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa ta bayyana dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke zancen karban Rancen dala biliyan 3 daga Bankin Duniya.

Zainab ta jadada da cewa za a yi amfani da kudin ne domin kawo sauyi a bangaren samar da wutar lantarki.

4. Majalisar Dattawa Ta Hana Manema Labarai Daga shiga Taron Tsarin Kasafin Kudi

A ranar Alhamis din nan da ta gabata ne aka fara ba da kariya ga kasafin kudin shekara ta 2020 ga ma’aikatun, sassan, da kuma ma’aikatu (MDAs).

Naija News ta fahimta da cewa Majalisar Dattawar ta hana duk wasu manema labarai da suka halarci taron sirin kin shiga taron.

5. ‘Yan Shi’a na Shirin Fita sabuwar Zanga-Zanga a dukan Kasa

Wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun bayyana shirye-shiryen fara taron shekara da shekara da suka saba yi ta Arba’een a kasar, a ranar Asabar din nan.

Naija News ta bayar da rahoton cewa IMN ta ba da tabbacin cewa hidimar tasu za ta kasance cikin lumana kuma ba ta da duk wani yunƙurin wargaza tafiya da fitar mutane a kan hanya a ranar.

6. Shugaba Buhari da Gwamnonin Jihohi sun Gana a Aso Rock

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnonin jihohi tara masu samar da Arzikin Mai a kasar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Gwamna Seriake Dickson, Gwamnan Jihar Bayelsa a yayin zantawa da manema labarai bayan ganawar a fadar Shugaban kasa, ya fada da cewa abubuwan da aka tattauna sun hada da zancen tsaro, tattalin arziki da ci gaban jihohinsu daban-daban.

7. Shugaba Buhari ya yi Furci game da Gobarar Wuta a Onitsha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa wadanda gobarar wuta ya lallace kadarorin su, da barnan mallaka harma da dauke rayuwansu a Onitsha.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa wata mumunar gobarar wuta ta kama babban kasuwar Onitsha ranar Laraba bayan da wata Motar Tanki da ke dauke da Man Fetur ya fashe.

8. Gwamnatin Tarayyar Najeriya na batun karban Haraji Akan Kayan Lemu

A yayin kokarin shigar da kudade a kasa, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fito da sabon tsarin sa biyan haraji kan kayan lemu iri-iri da ake sha a kasar.

Naija News ta fahimci cewa Ministar Kudi ta Najeriya, Misis Zainab Ahmed wacce ta sanar da hakan ta ce gwamnatin tana aiki kan yadda za ta kara inganta hanyoyin samun kudade a kasar.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa