Boko Haram: ISWAP sun Kashe Sojojin Najeriya Biyar a Borno

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa ‘Yan kungiyar Islamic State West Africa County (ISWAP) sun kashe a kalla sojojin Najeriya hudu da wani mayaki a cikin jihar Borno.

A cewar majiyoyin tsaro da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Lahadi, ya bayyana da cewa fadar ya barke ne a yammacin Asabar a yayin da sojoji suka yi wa wani ayarin ‘yan kungiyar ISWAP – wanda suka tashi daga kungiyar Boko Haram – kusa da kauyen Jakana, mai nisan kilomita 42 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun rushe wata rukunin ‘yan Boko Haram da ke a Boboshe, a karkarar da Dajin Sambisa ta ke a nan Borno.

An bayyana da cewa wannan wajen da Sojojin suka rusa da Bam wajen hadin taro ne ga ‘yan ta’addan Boko Haram.