Connect with us

Uncategorized

Membobin NYSC Zasu Fara Karban Mafi karancin Albashi na N30,000 – FG

Published

on

at

advertisement

Mambobin Kungiyar Matasa da ke Bautar Kasa (NYSC) za su ji daɗin sabon mafi karancin albashi na N30,000, in ji Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News na ba da rahoton kamar yadda ministan matasa da wasanni ya sanar da hakan a cikin wata sakon da ya wallafa a shafin yanar gizon Twitter, da yammacin ranar Laraba, 23 ga Oktoba.

Shafin Naija News ta Turanci ta sanar a baya da cewa Hukumar da ke kula da gudanarwan Hidimar NYSC ta kasa ta fara shigar da sunan masu zuwa bautar kasa ta shekarar 2019.

Dangwala wannan layin don samun sanarwan da kuma karin bayani akan yadda za a iya shigar da suna ga hidimar bautar kasa ta ‘Batch C a 2019’.