Connect with us

Labaran Najeriya

Sabuwa: Shugaba Buhari zai Ziyarci kasar Landan har Tsawon Kwanaki 17

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasar Najeriya a yau (Litinin), a wata ziyarar aiki da zai yi zuwa Masarautar Saudi Arabiya don halartar Babban Taron Hadin gwiwar Kawo Zuba Jari (FII) a Riyadh.

Kamar yadda aka sanar a labarai a baya a Naija News, an ruwaito da cewa Shugaba Buhari zai yi tattaunawa ta biyu tare da Mai Girma Sarki Salman da Mai Girma Sarki Abdullah ll na Jordan a yayin taron da zasu yi a Saudiya.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Babban Taron zai kunshi taken “Abin da ke Gaba ga Afirka: Ta yaya Zuba Jari da Kasuwanci za su canza yankunan kasar, Tayaya za a karfafa Tattalin arziki?”.

Taron ta hada ne da shugaban kasar Kenya, Congo-Brazzaville and Burkina Faso da dai sauransu.

An kuma bada tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari bayan taron zai tafi kasar London, a United Kingdom don wata ziyarar Siri.

Naija News ta samu tabbacin wannan sabuwar tafiyar Buhari ne a yau Litini, 28 ga Oktoba, a wata sanarwa da Mista Femi Adesina, mataimakin musanman wajen bada shawarwari ga shugab Buhari ya bayar, da cewa “shugaban zai halarci wata taro tun daga ranar Asabar, 2 ga Nuwamba zuwa ranar 17 ga Nuwamba 2019, kasar UK.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Buhari ya Nada wa Matarsa Aisha Buhari Mataimaka 6 don taimaka mata ga ayukanta.