Connect with us

Labaran Najeriya

Shehu Sani Ya Bayyana zabin sa ga Shugabancin Kasar Najeriya a zabe ta gaba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon sanata mai wakilcir Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ba da sanarwar sauya shugabancin kasa zuwa yankin Kudancin kasar nan a 2023.

Sani ya yi nuni da cewa rashin ba wasu yankuna a kasar damar shugabancin shekara ta 2023 na iya haifar da rikici a siyasan kasar da kuma kawo matsaloli a Najeriya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shehu Sani ya gargadi Arewa da su manta da zancen shugabancin kasar Najeriya daga Arewacin kasar a zaben shugaban kasa ta 2023 da ke a gaba.

“Ku manta da batun neman wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin Najeriya a zaben shugaban kasa ta 2023” inji shi. 

KARANTA WANNAN KUMA; Kannywood – Muna da kudurin Fita takaran zabe nan gaba – inji Ali Nuhu