Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 31 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 31 ga Watan Oktoba, 2019

1. Kotun Koli ta Ba da hukuncin karshe a Karar da Atiku ya yiwa Buhari

Kotun kolin a ranar Laraba ta yi watsi da karar da Atiku Abubakar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka shigar kan cin nasarar zaben shugaban kasa da Muhammadu Buhari, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayi.

Kotun koli, ta yanke hukunci a kan PDP da dan takararta, Atiku da kuma tabbatar da nasarar Buhari akan cewa karar da Atiku da PDP suka yi bai cancanta.

2. Kotu ta umurci Majalisar Jihar Legas da ta dakatar da binciken Ambode

Wata babbar kotu da ke zaune a Jihar Legas ta umarci Kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa da sauran membobin kwamitin da su dakatar da duk wani bincike da ake yi ga kan sayen motocin bas 820.

Naija News ta fahimci cewa Justice Y.A. Adesanya ya yanke hukuncin ne bisa ga goyon bayan tsohon gwamna Legas, Mista Akinwunmi Ambode wanda ya yi karar majalisar dokokin jihar Legas a gaban kotu bisa zargin karya da bayanan karya da kuma karkatar da dukiyar jama’a da ake da shi.

3. Atiku yayi Magana kan kayen da ya sha a Kotun Koli

Dan takarar Shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga hukuncin da Kotun koli ta yanka, wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar All Progressives Congress a zaben 2019.

Babban alkalin Najeriya, CJN, Tanko Mohammed a cikin hukuncin nasa ya ce, “Mun bincika dukkan takaitattun bayanai da kuma nune-nune sama da makwanni biyu.

4. Yadda PDP ta maida martani ga nasarar Buhari a Kotun Koli

Shugaban tarayyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus, ya mayar da martani ga nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a Kotun Koli.

Naija News ta ruwaito cewa Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe a ranar Laraba kan karar da Atiku Abubakar da Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi a kan nasarar zaben Shugaba Buhari, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2019.

5. Mobolaji Johnson Ya Mutu!

Tsohon Gwamna da kuma Gwamnan farko a mulkin Soja ta jihar Legas, Brig-Gen. Mobolaji Olufunso Johnson ya mutu.

Tabbacin hakan ya bayyana ne ta bakin dansa, Deji.

6. INEC na Shirin Samar da Hukumar EFCC, ICPC don hana Masu Zaluncin Zabe A Kogi da kuma Yankin Bayelsa

Hukumar Gudanar da Zaben kasa ta bayyana cewa za ta tura Ma’aikatan Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa Ta’annati da kuma Yaki da Cin Hanci da Rashawa, hade da sauran hukumomin da ke yaki da laifuka da miyagun halaye ga Jihar Kogi da Bayelsa don kamun masu sayen kuri’u a lokacin zaben gwamnoni na Nuwamba 16 a jihohin.

Hukumar zaben a ranar Talata ta ce za a sanya dukkan jami’anta da ma’aikatan zabe a karkashin rantsar da su a hukumance, da kuma sa jam’iyyun siyasa su rattaba hannu ga takarda don tabbatar da zabe mara makirci da tashin hankali.

7. Shugaba Buhari ya mayarda martani yayin da Kotun Koli ta Tabbatar da Zabe

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya gode wa ‘yan Najeriya bisa goyon baya da aka ba shi don sake jagorancin kasar nan zuwa ga shekaru hudu.

Naija News ta ruwaito cewa Kotun Koli ta yanke hukunci a ranar Laraba da ta shigar da karar da Atiku Abubakar da Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi a kan nasarar zaben Shugaba Buhari, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

8. Shugaban kasar Ghana ya Mayar da Martani game da rufe Bodar Kasa

Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya mayar da martani ga shawarar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke na rufe bodar kasarta don shigo da kaya daga kasashen waje.

Akufo-Addo yayin magana a karon farko kan batun rufe bodar da shugabancin Najeriya ta yi ya fada da cewa, matakin zai iya jawo illa ga tsarin hadewar ECOWAS.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa