Labaran Najeriya
Kullewar Boda: Karanta Gargadin Shugaba Muhammadu Buhari Ga ‘Yan Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa ‘yan Najeriya dalilin da ya sa ya kamata su hanzarta ga yin amfani da kayayyakin da aka kerawa cikin Kasar.
Shugaban kasar, Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su amince da diban muhinmancin saye da amfani da kayayyaki da ake kira a kasar don karfafa ta da taimaka wajen yawaitar da tattalin arzikin ta.
Buhari ya fadi hakan ne yayin jawabin sa na farko a yayin bude bikin gabatar da Kasuwanci na kasa da kasa a shekarar 2019 da aka yi a birnin Legas.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din makon da ta gabata, a wata ziyara da ya kai a kasar Saudiyya, ya bayyana cewa Najeriya na fatan ta rungumi sabon salo na hadin gwiwar Afirka da kasar Rasha don sake farfado da dangantakar Najeriya da Rasha.