Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 5 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 5 ga Watan Nuwamba, 2019
1. Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar takaita kashe was kudade
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga dokar kudin dala biliyan 1.4 na PSC da ake nema don inganta zurfin kwangilar samar da kayayyaki da ke karkashin kasa (DOIBPSC).
Naija News ta fahimta da cewa kudirin na da nufin gyara dokar ne ta hanyar da gwamnatin tarayya za ta samu fa’idojinta ta hanyar duba tsarin raba kudin.
2. Kotu ta Tsige Shugaban Majalisa Mai Rinjaye a Kano, Alhassan Doguwa
A ranar Litini da ta gabata, kotun daukaka kara da ke zaune a Kaduna ta sallami Shugaban majalisar wakilai mai rinjayi, Mallam Alhassan Ado Doguwa a Kano.
An zabi Doguwa ne a dandamalin All Progressives Congress domin wakiltar mazabar tarayya ta Tudunwada / Doguwa na jihar Kano.
3. Sowore ya Ki Amince da Taimakon Manzo Suleman
Mista Omoyele Sowore, ma’aikacin gidan jaridar Sahara, ya ki amince da taimakon da jagora da babban Faston ‘Omega Fire Ministry International’, Manzo Johnson Suleman, yayi don tabbatar da belin sa.
Kungiyar lauyoyi da ke wakilcin belin Sowore, musamman babban lauyansa Inibehe Effiong, ya fada wa manema labarai cewa Suleman bai cancanci ya tsaya wa Sowore ba saboda kotu ta bayyana a fili cewa lallai duk wanda zai taimaka da tsaya masa dole ne ya zama mai iko da zama a Abuja.
4. Kogi Guber: INEC ta Samar da Kwamishinoni uku na kasa da REC Bakwai Hidimar Zabe
Shugaban Hukumar Gudanar da Hidimar zaben kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya amince da tura wasu kwamishinoni uku na hukumar da kuma kwamishinonin Zabe bakwai, gabanin zaben gwamna a jihar Kogi.
Shugaban, Ma’aikatar Ilimi da Sanar da Jama’a, Ahmed Biambo, ne ya bayyana hakan a ofishin Lokoja ranar Litinin.
5. Yadda Okorocha Ya Ba Ni Kudi Dala $2m Don Juya Sakamakon Zabe – Gulak
Shugaban kwamitin da ke jagorantar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na zaben gwamnonin jihohin Imo ta shekarar 2019, Ahmed Gulak ya zargi Rochas Okorocha da yin niyyar siyan zaben jihar.
Gulak a cikin wata sabuwar tuhumar da ake ma Okorocha, ya bayyana da cewa tsohon Gwamnan ya yi niya da neman sa da cin hanci da rashawa don tabbatar da cewa sakamakon zaben fitar da gwani ya kawo karshe ga zababben dan takarar sa, Uche Nwosu.
6. Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Dalilin Tafiyar Shugaba Buhari
Fadar shugaban kasa ta baiyana yawan tafiye-tafiyen kasashen waje da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi, a cewa Najeriya na bukatar irin wadannan tafiye-tafiye.
Da yake bayyana dalilan tafiyar, Garba Shehu, Babban Mataimaki na Musamman kan Kafafen yada labarai da sanarwa ga shugaban ya ce tafiye-tafiyen na afkuwa ne don gyara fasalin kasar nan da kuma sayar da damar tattalin arziki ga masu son saka hannun jari.
7. Kogi Guber: PDP Ta zargi Gwamna Bello Da Shirya Tsananci ga Shugabannin adawa
Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Kogi ta bayyana wani shirin zargin da gwamnan jihar, Yahaya Bello ke yi don gudanar da makirci da lallace zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba.
Jam’iyyar adawar ta zargi gwamnan jihar da neman tsananta wa shugabannin jam’iyyarsa gabanin babban zaben da ke gabatowa.
8. Mafi karancin albashi: Kungiyar Kwadago na barazana ga Gwamnonin Jihohi kan aiwatarwa
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi kira da a tsige gwamnonin jihohi wadanda ba a shirye suke ba da biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikata.
Naija News ta gane da cewa Kungiyar na har ila yau yin kira ga Majalisun Dokokin Jiha da su goyi bayan kiran da ma’aikata ke yi kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
Ka sami kari da Cikkaken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa