Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari Bai Raina Osinbajo Don Yin Tafiya Ba Tare da Isar da Damar Shugabanci a Gareshi ba – Omoworare

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanata Babajide Omoworare, Babban Mataimakin Shugaban Kasa na Musamman ga abin da ya shafi Majalisar Dattawar kasa, a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa Shugaban kasar, Muhammadu Buhari bai raina ko kuma yi watsi da ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ba, don fita daga Najeriya ba tare da bada damar ci gaba da shugabanci da wakilci ba ga mataimakin nasa, musanman a hidimar da ta shafin Majalisar kasa.

Sanatan a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya, Abuja, tare da abokin aikin sa a Majalisar Wakilai, Umar El-Yakub, ya bayyana cewa Shugaban kasa na iya aiwatar da aikin sa daga ko ina a fadin duniya.

Ga bayanin kamar haka;

“Sabanin cece-kuce da jita-jitan da wasu mutane da kungiyoyi ke yi da ikirari, Shugaban kasar ba wai yayi tawaye ko nuna watsi da ofishin Mataimakin Shugaban kasa ba ne. Ba gaskiya ba ne hakan, kuma bai da wata dalili ko riba ga yin hakan,” inji shi.

“Bana yin tsanmanin cewa akwai wata dalili ko manufa da zai sa ayiwa ofishin Mataimakin Shugaban kasar haka.”

Ya kara da cewa, lokacin da kawai za a iya tuhumar shugaban kasar da irin hakan itace kawai lokacin da Shugaban kasar ba shi da lafiya kuma ya kasa tattaunawa da Majalisar Dokoki ta kasa, har kuma ga kin bayar da damar hakan ga mataimakin sa.

Mista Babajide yayi nuni da lokacin da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ba shi da lafiya kuma ya kasa ga iya sadarwa ko isar da wata wasika ga Majalisar Dokokin kasar.

KARANTA WANNAN KUMA; Gargadin Shugaba Muhammadu Buhari Ga ‘Yan Najeriya.