Majalisar Dattawa ta Tabbatar da Tsoho A Matsayin Babban Alkali | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Majalisar Dattawa ta Tabbatar da Tsoho A Matsayin Babban Alkali

Published

Majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar da nadin Mai shari’a John Tsoho a matsayin Babban Alkalin Kotun Tarayya ta hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

Tabbatarwar ta biyo ne bayan rahoton da Sanata Michael Bamidele, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa a bangaren Shari’a, Mai Kare Hakkin Dan Adam da Batutuwan Shari’a, ya bayar da shawarar tabbatar da nadin Tsoho.

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa shugaban Muhammadu Buhari ya mikar da sunan mai shari’a John Tsoho ga Majalisar Dattawa don dubawa da tabbatar dashi a matsayin babban alkalin babbar kotun tarayyar kasar.

Naija News ta bayar da rahoton ne da tabbacin cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aika wa majalisar dattijan Najeriya wanda shugaban majalisar zartarwar kasar, Ahmad Lawan ya karanta a ranar Talata, 29 ga Oktoba 2019.

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.