Connect with us

Uncategorized

PDP Ta Zargi Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da Shirin Kame Dino Melaye

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Jam’iyyar Adawar kasa, PDP ta zargi Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da darakta-janar na kamfen din sa da shirin kamu da tsare Sanata Dino Melaye gabanin zaben ranar 16 ga Nuwamba.

Jam’iyyar adawar ta lura da cewa an gabatar da shirin ne a ranar Litinin yayin wani taro da aka yi a gidan Gwamnatin Jihar.

Mataimakin musanman ga yada labarai na Sanata Melaye, Gideon Ayodele, a ranar Talata ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Kogi da manajan kamfen dinsa sun kammala wata shirin tabbatar da cewa an kama Melaye kuma an tsare shi kafin zaben kujerar gwamna a Jihar da ke gabatowa.

Sanarwar tana kamar haka;

“Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta yi kira ga jama’ar Kogi West Senatorial District da masu jefa kuri’a duka da su yi adawa da duk wani yunkuri na kwace musu ‘yancinsu na zaban wadanda suke so a zabukan.”

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Darakta Janar na Gwamna Bello wajen yada labarai, Kingsley Fanwo, ya fada da cewa ba aikin gwamna bane na kama masu laifi.

Ya ce, “Gwamnan ba shi da muradin kama kowa, har ma da Dino Melaye, saboda babu bukatar hakan. Ya rigaya da fadi zaben, baya kamfen kuma tunda bai da abin fada wa mutane. ”