Connect with us

Uncategorized

Eid-El-Maulud: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutun Mauludi {Duba Kwanan Wata)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu ta Jama’a a bikin tunawa da zagayowar Eid-El-Maulud wanda ya kasance ranar tunawa da haihuwar manzon Allah Muhammad.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar cikin gidan, Mista Mohammed Manga ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Alhamis a birnin tarayya, Abuja, a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.

A cikan sanarwar, An taya muminai musulmai murnar bikin tare da umurce su da su zauna cikin kyawawan halaye da koyarwar Annabi.

A cewarsa Aregbesola, kwaikwayon kyawawan halayen Annabi na kauna, karfin hali da juriya zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar, idan har anbi da biyayya.

Ya kuwa nuna gamsuwarsa da cewa kalubalen da ke addabar kasar Najeriya a halin yanzu zai kawo ga karshe; don haka ya yi kira ga ‘yan Najeriya duka da su mayar da hankali da jajircewa.

Ya ba da tabbacin cewa a irin wadatar da albarkatun da kasar Najeriya ke da ita, “lallai ba da jimawa ba Najeriya za ta shiga cikin jerin ƙasashe da ke cike da Ci gaba.”

“da soyayya, sadaukarwa, hakuri da kishin kasa, tabbas za mu gina Najeriya mafi girma da wadata.” inji Aregbesola.

Ministan ya sake jaddada aniyar Gwamnati na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga dukkan ‘yan Najeriya.

KARANTA WANNAN KUMA; Hotunan Fati Washa da Masoya Suka yi Allah Wadai da shi