Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 7 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 7 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Dakatar da Ma’aikata 35 A Ofishin Osinbajo

‘Yan kwanaki kadan bayan korafin da wasu’ yan Najeriya ke yi kan Batun Dokar Tsari ta Inland Basin Production wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a cikin dokar a London, Ana zargin cewa shugaban ya sake daukar wani mataki mai muni a ofishin Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Naija News ta samu labari daga wani rahoto da aka wallafa a kan jaridar Daily Nigerian cewa Shugaban wanda yake a Burtaniya don wata ziyarar kai tsaye ya kori ma’aikatan mataimakansa 35.

2. NASS na bincike akan Chinda, da Sauran Shugabannin Jam’iyyar PDP

Majalisar wakilai a ranar Laraba ta fara bincike kan mambobi hudu wadanda aka bayyana da zaman shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar.

Naija News ta gane da sunana wadanda ake binciken da Hon. Kingsley Chinda, Toby Okechukwu, Umar Barde da Muraina Ajibola.

3. Sowore da Bakare Sun Cinma Yanayin Beli – Falana

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana, a ranar Laraba, ya fada wa babbar kotun tarayya, a Abuja cewa mawallafin jaridar Sahara Reporter, Omoyele Sowore da abokin kararsa, Olawale Bakare sun cika sharuddan belin su.

Lauyan kare hakkin dan adam din ya bayyana cewa za a saki  Sowore da Bakare wadanda aka katange akan laifin halin neman tayar da tanzoma a kasa.

4. Dalilin da yasa Abba Kyari yafi Osinbajo Muhinmaci – Inji Dan Majalisa

Dan majalisa mai wakiltar mazabar karamar hukumar Egbeda / Ona, Akin Alabi, ya mayar da martani game da rahoton da aka gabatar na cewa Shugaban Ma’aikatar Shugaba Muhammadu Buhari, Abba Kyari, ya yi tafiya zuwa kasar Landan don neman sanya hannun Shugaban kasa a wata doka.

Alabi a ra’ayinsa kan lamarin ya bayyana da cewa a tsarin shugabanci da ake yi a Najeriya, ofishin Babban Hafsan ya fi karfin Ofishin Mataimakin Shugaban kasa.

5. Edo 2020: Shugabannin APC sun Mara Bayan Obaseki ga Tikitin Kujerar Gwamna

Shugabannin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Jihar Edo sun karɓi Gwamna Godwin Obaseki a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamna ta 2020.

Naija News ta bayar da rahoton cewa shugabannin daga kananan hukumomi 18 na jihar Edo sun goyi bayan Obaseki a yayin ganawarsu da gwamnan a gidan Gwamnati a garin Benin City.

6. Buhari bai raunana Osinbajo ba – Omoworare

Sanata Babajide Omoworare, Babban Mataimakin Shugaban Kasa na Musamman ga abin da ya shafi Majalisar Dattawar kasa, a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa Shugaban kasar, Muhammadu Buhari bai raina ko kuma yi watsi da ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ba, don fita daga Najeriya ba tare da bada damar ci gaba da shugabanci da wakilci ba ga mataimakin nasa, musanman a hidimar da ta shafin Majalisar kasa.

Sanatan a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya, Abuja, tare da abokin aikin sa a Majalisar Wakilai, Umar El-Yakub, ya bayyana cewa Shugaban kasa na iya aiwatar da aikin sa daga ko ina a fadin duniya.

7. Majalisar Dattawan Najeriya ta sake Bayyana Doka don Magance Labaran Karya

Halin Makirci akan layin yanar gizo, labarai na karya da kalaman batanci yana daya daga cikin mahimman fassarorin fasalin al’adun Najeriya wadanda suka gurbata kimar al’umma a Afirka.

Naija News ta fahimci cewa wadannan matakan sun sanya gwamnatin Najeriya da fara aiwatar da batun binciken layukan sadarwa ta yanar gizo a kasar da tsara amfani da kafofin watsa labaru.

8. Kotun daukaka kara ta Tsige Adeyeye na APC

Kotun daukaka karar ta tsige Kakakin yada yawun Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Dayo Adeyeye na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.

Naija News ta ba da rahoton cewa Kotun daukaka karar ta yanke wannan hukunci ne a ranar Laraba a Kaduna, arewacin Najeriya, bayan sauya fasalin farko da aka yi daga Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

9. Amurka ta gargadi Ba-Amurke da kada su ziyarci Jihohi 14 a Kasar Najeriya

Kasar Amurka ta bayar da gargadin tafiye-tafiye ga ‘yan kasarta game da ziyartar jihohi goma sha hudu a Najeriya yayin da ta lisafta jihohin da “Yankuna masu hadarin gaske.”

An fitar da gargaɗin ne a wata bangaren labarai ta hannun Ofishin Harkokin Jakadanci.

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a shafin Naija News Hausa