Uncategorized
An Kame Wani Mutumi Mai Shekaru 42 A Yayin Sayar da Dansa a Jihar Nasarawa
Naija News Hausa ta karbi rahoron kame wani mutum mai shekaru 42 da haihuwa da aka yi, wanda aka zargeshi da kokarin sayar da dansa mai shekara uku da haifuwa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa kan yawar kudi miliyan N5.
Kwamandan rundunar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) wadda aka fi sani da suna ‘Civil Defence’ Mista Mohammed Mahmoud-Fari ya bayyanawa manema labarai da cewa, sun kama wanda ake zargin ne a wani samamen da jami’an rundunar suka yi bayan da suka karbi wata likin bayanai game da niyyar siyarwa daga wani mazauni.
A bayanin Mahmoud, ya bayyana da cewa;
“Jami’an mu sun karbi rahoton matakin da mahaifin yaron ya dauka a sirance, suka kuwa fara tattaunawa da shi a matsayin zasu sayi yaron daga hannunsa, inda ya bayyana masu da cewa zai sayar da shi a kan kudi Naira miliyan biyar.”
“Ya nuna da cewa yana son ya karbi kudin ne a warware cikin jikka, ana cikin hirar hakan ne muka kuwa kama shi a garin Lafiya,” in ji Mahmoud-Fari.
Mahmoud ya bayyana cewa mutumin da aka kama da zargin sayar da dansa mazuni ne a karamar hukumar Obi, yana kuwa da mata biyar da ‘ya’ya 23, wadanda a cikinsu ya riga ya sayar da diya guda tun a baya.
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa da amince da laifinsa kuma, ya danganta matakin da ya dauka akan yanayin wahalar tallauci da ake fuskanta a kasar, a kuma cewa ya sayar da dan nasa ne domin ya samu kudin da zai kula da sauran diyansa da matansa biyar.
KARANTA WANNAN KUMA; Cututtuka da Namijin Goro ke Iya Warkas wa a jikin Dan Adam.