Uncategorized
Jihar Bauchi ta shiga Mawuyacin Hali A Yayin Da Mutane 29 Suka Mutu da Cizon Sauro
Cizon Sauro ya dauke Rayuka akalla 29 a Jihar Bauchi
An ruwaito a labarai da cewa Cutar zazzabin cizon sauro, wata cuta mai saurin yaduwa sakamakon cizon sauro ta kashe mutane 29 a jihar Bauchi.
Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa wata sanarwa da aka bayar daga bakin Dokta Rilwanu Mohammed, shugaban Babbar Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Bauchi (BSPHDA), a yayin bada adadin wadanda suka mutu a ranar Alhamis.
Ya ce;
“binciken da muka yi ya bayyana mutane 224 da ke kame da ciwon, sannan kuma mutane 29 sun mutu. “Mutane 24 a karamar hukumar Alkaleri, biyu a karamar hukumar Bauchi, 1 a karamar hukumar Darazo da biyu kuma a karamar hukumar Ningi.”
“an fara ne da gano alamar cutar a yankin karamar hukumar Alkaleri a watan Satumbar da ta gabata, mun kuwa dauki matakai da tabbatar da cewa an hana cutar da yaduwar,” Inji Shi.
Ya kara da cewa wannan shi yasa gwamnatin jihar ta yi iya kokarin ta ta hanyar yin allurar rigakafi ga mutanen da ke zaune a yankunan don dakile yaduwar kamu da cutar a kananan hukumomin.
“A yanzu haka, an riga an ba da alluran rigakafi 500,000 a Alkaleri, kuma muna tsammanin za a gudanar da allurar rigakafin 600,000 a cikin yankin Ningi,” in ji shi.
Ciyaman na hukumar BSPHDA ya kara bada haske da cewa lallai cutar ‘Yellow Fever’ ba cuta bace mai yaduwa don hadewa da masu cutar ba, amma da cewa za a iya kamuwa ne da cutar kawai ta hanyar cizon sauro.
Ya kuma gargadi mazauna da cewa kada su yi jinkiri wajen sanar da duk wata alamar yaduwar cuta da suka iya gane da ita a yankin su.