Uncategorized
Dalili na da Kwanci Da Maza 15 a Kowace Rana – Wata ‘Yar Shekara 15
Abin Mamaki da Tausayi a yayin da Karamar Yarinya ke Kwanci da Maza 15 a Kowace Rana
Naija News Hausa ta ci karo da labarain wata ‘yar karamar yarinya da aka bayyana da kwanci da maza a kullum don biyan bashi. Yarinyar mai shekara 15 kacal da haifuwa, wacce ke zaune a gararamba a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ta bayyana irin mumunar halin da ta iske kanta.
Ngozi, kamar yadda aka bayar da sunanta a kamfanin dilancin labarai ta BBC Hausa ta kwashe watanni tana fuskanta wannan mumunar halin ne da ta iske kanta a wani otel da ke unguwar Lugbe a Abuja.
Rahoto ya bayyana da cea Ngozi ta fada wannan hali ne bayan da wata makwabtciyarsu a wani kauye da ke a jihar Anambra ta yi mata alkawarin taimaka mata da daukar nauyin biyan kudin makaranta idan har ta bita zuwa birnin Abuja.
A yayin mayar da martani akan al’amarin, Ngozi fada da cewa;
“Madam takan umarce ni dole da sanya guntun siket da karamar riga. Nakan kwanta da maza 15 a kan naira 1000 kan kowane mutum, nakan hada a kalla 15,000 a kowace rana domin biyan ta bashi.” Inji bayanin yarinyar da ta bayar ga hukumar tsaro.
A bisa bayanin Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya (NAPTIP), ta bayyana da cewa akwai akalla kashi 75 na yara irin su Ngozi da ake fatauci daga wata jiha zuwa wata, a Najeriya, sukan fada ne a hannun miyagun mutanen.
Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa